A bisa al'ada, a lokutan bikin sallah akan hada taron zumunci na kungiyar tsaffin dalibai, daga Firamare har izuwa high institutions.
Idan baka halarta, ya kamata kana halarta. Wasu saboda zumunci, an zama tamkar 'yan uwa na jini... ana zumunci, ana taimakekkeniya...
Sai dai wata dabi'a maras kyau da ya kamata a gyara, ita ce, auna nasarorin juna a rayuwa. Wani ya samu AIKIN GWAMNATI, wasu zama Dan Kasuwa, wani yana KARATU A BABBAR MAKARANTA, wani ya zama YARON WANI BABBA (Special Assistant), wani ya yi AURE... wani kuma har yanzu rayuwa bata ba shi kasonsa ba... gwargwadon nasarar a rayuwa, gwargwadon kimarka a wajen.
Taron OLD BOYS, ko ALMA MATER, taro na SADA ZUMUNCI, ba taron gasar nuna nasara ba, SHI YA WASU BA SA SON ZUWA. Wanda kake gani ba komai ba a yau, ta iyu gobe ya zama mai taimakonka a rayuwa.
✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Dhul-Hijjah, 1443AH
7th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

0 Comments