Farfesu



 • Kalmar FARFESU, asali daga 'Pepper Soup' (kalmar Turanci) aka aro ta.


FARFE = Pepper

SU = Soup


A Hausance, Farfesu (Peppersoup), ana ƙiransa da DABGE ko DAGE-DAGE.


• Kalmar BIREDI kam, kai tsaye daga Turanci aka aro ta. A Hausance, BREAD, ana ƙiransa da MUMMUKI (bugun ƙato).


Loanwords, shi ne aron wata kalma, daga wani yare, ba tare da an jinkirta furucinta ko canja wani sashe nata sosai ba (Otto, 1964).


Ba gazawa ba ne, ko ƙarancin kalmomi ke sa wani yare yin aron kalma daga wani yaren ba, a'a; babu yaren da ba ya aron kalma. TURANCI (English) shi ne ma yaren da ya fi kowanne yare a duniya aron kalmomi (Diep, 2014). Kyle (2020) Ya ce, fiye da 75% na kalmomin INGILISHI ko TURANCI, an aro su ne daga wasu yarukan, mafi yawanci daga ciki, daga Greek, Latin, French da sauransu.


A ci FARFESU da MUMMUKI lafiya. Fatan za a ci lagwada lafiya tare da taka-tsantsan. Allah Ya mana tsari da tsuyewar ciki, amin.


✍️ Aliyu M. Ahmad

11th Dhul-Hijjah, 1443AH

10th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #Linguistics #Hausa #EidMubarak

Post a Comment

0 Comments