A ɗabi’a! Manomi sai ya ɗauki lokaci yana wahala, kafin shuka ta fito, ta girma, ya girbe, ya amfana. Haka! Mace mai ciki sai ta yi rainon ciki na watanni, kafin ya isa a haifo shi. Matafiyi, sai ya motsa a hankali, a hankali, kafin ya isa inda yake son zuwa. Kai! Hatta ɗanye abin ci, sai an jira ya nuna a saman wuta, kafin a sauke a sa baka… BA GAGGAWA, a ɗabi’a (nature), sai an bi komai ta wani matakin.
Haka yake! A duk lokacin da ka yi addu'a, ka roƙi Ubangiji wata buƙata, misali; idan kana neman lafiya, kuɗi, aure, haihuwa, mulki, rufin asiri…
1. …ba wai don ka roƙi kuɗi, za a zubo ma shi (kuɗin) daga sama ba ne, a'a; ko ka ga, kuɗi yana ta shigo ma ta ko’ina… a'a, sai an samu sanadin zuwan kuɗin tukun; tashi zaka yi ka nema, tare da bin duk wani mataki na nema, sai Allah Ya sauƙaƙa ma hanyar neman.
Ba a rana ɗaya ƊANGOTE ya zama ƊANGOTE ba, da ƙaramin jari ya fara, a hankali… hakanan ba rana ɗaya PROFESSOR ya zama PROF ba, daga ASSISTANT GRADUATE yake farawa… ba rana ɗaya DIRECTOR ko PERMANENT SECRETARY ya zama DG ko PS ba, duk daga matakin ƙasa suke farawa.
2. Idan baka da lafiya, ba kwanciya zaka yi ba kana jiran sauƙi ba, magani zaka tashi ka nema, sai Allah Ya sanya ma waraka cikin magani.
3. Idan aure kake nema, duk wani sanadi da zai tabbatar da auren zaka tanada, neman kudi, mutunci, neman soyayya da wahalhalunta, juriya, hakuri… sai Allah Ya tabbatar da alherinsa cikin neman auranka.
4. Idan mulki kake nema, duk wani abu da ake yi domin samun mulki, tsara duk wani shiri domin samun goyon baya, sai ka gama da addu’a, sai Al-Maliku ya baka mulki.
5. Idan rufin asiri kake nema, sai ka nemi sana’a, ka ƙauracewa duk abin da zubda ma da mutunci a idon duniya, a fili da ɓoye, Allah ba zai ƙaddara ka tozarta ba.
Addu’a da aiki, tamkar tsuntsu ne mai fika-fikai biyu, ka yi aiki tukuru, ka yi addu’a, da sannu zaka cimma burinka… BA A GAGGAWA! Fafala ce daga Allah kuma, Ya azurta cikin kankanin lokaci, ba wahala.
✍️ Aliyu M. Ahmad
12th Dhul-Hijjah, 1443AH
11th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Addua #Hausa

0 Comments