Social Media Identity

 



In da mun sun san posting da muke a media, har na BARKWANCI zai bibiyi rayuwarmu ta zahiri ko a gaba wajen neman aure ko aiki, da ba mu maida hankali kan shiririta ba. Duk abin da muke, muna bayyanawa duniya kanmu ne (self-presentation).


A wasu wuraren, har profile na social media ake bibiya na mutum domin tabbatar da nagartarsa kafin samun gurbin aiki ko wata dama.


Social media sabon shafin bada bayananka (résumé) ne, ra'ayinka da tunaninka.. Ta dalilin dandalin social media, wasu sun samu aikin yi, wasu sun rasa aiki, wasu sun kasa samu, wasu an tsayar da su gaban shari'a, wasu an ɗaure su, wasu an musu tayin aure, wasu an hana su aure...


Misali! Wani ya yi posting da sunan barkwanci wai:


"DA YA ZAUNA DA TAULACI, GWAMMA YA SAMI DAMA, YANA TA ZIRGA-ZIRGA ZUWA EFCC".


Ba ya tunanin za a screenshot a ajiye, a yi amfani da shi lokacin da Allah Ya ƙaddara zai fito neman wata kujera ta siyasa a gaba?


Barkwanci da laifi ba ne, a yi wasa, a yi raha, amma a kiyaye amfani da kalmomin batsa, manyan laifuka, mujahara, misinformation, disinformation... KAR KA ƊAUKA DA WASA, domin kalmominka za su farauce ka, ko anan duniya, ko a lahira.


MUTUM MAI HANKALI shi wanda ya san abin da ya kamata ya furta na magana. MUTUM MAI TUNANI kuwa, shi ne wanda yake auna ko ya dace ya furta magana KO yayi shiru (saboda da gudun abin da zai JE ya ZO).


NO NEED TO TELL THE WORLD WHO YOU ARE, YOUR PRESENTATION SAYS IT ALOT. SOCIAL MEDIA SHAPES OUR IDENTITY, USE IT WISELY PLEASE!


✍️ Aliyu M. Ahmad

26th Dhul-Hijjah, 1443AH

25th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani #SocialMedia

Post a Comment

0 Comments