Abu ne mai kyau ga ma'abocin amfani da social media, a kula da bayanansa na social media.Yanzu social media tamkar CV (Curriculum Viate/Resume) take ga mutum. Akwai wuraren aiyuka da yawa, musamman NGOs da suke buƙatar duba profile na social media naka, tunda ga suna, engagements, followings... duk ana dubawa.
Yana da kyau wajen amfani da suna, ka yi amfani da sunanka na asali (na yanka) a social media PROFILE.
A social media ana amfani da suna a mataki 2: 'USERNAME' da kuma 'PROFILE NAME'. Username a kowanne platform yana daga cikin 'login credentials', kai kaɗai za ka yi amfani da irinsa, ba za a sami (wani) mai irinsa ba, a kullum cikin ƙananan baki (lower case) ya ke, kuma babu 'space' a tsakanin kalmomi. Akwai shi a Gmail (𝘂𝘀𝗲𝗿𝗻𝗮𝗺𝗲@gmail.com), Facebook, Twitter, Instagram, Tiktok. Misali aliyumahmad11 a Facebook, fb.me/aliyumahmad11, ko aliyumahmad a Tiktok tiktok.com/aliyumahmad.
Shi kuma 'PROFILE NAME' shi ne sunan da ke bayyana a (fuskar) profile na mutum. Wannan akan iya samun mutane da yawa masu suna iri ɗaya, sannan akwai 'space(s)' a tsakanin kalmomi. Misali Aliyu M. Ahmad.
Idan kana amfani da suna mai 'abbreviation' misali ALIYU (M) AHMAD, wannan M ka sanya mata aya (full stop [.]), Aliyu M(.) Ahmad. Misali:
Aliyu M. Ahmad ✅
Aliyu M Ahmad ❌ (babu [.] a M)
Idan kuma a sunan, za ka rage (abbreviate) sunaye biyu ne, za ka rubuta harafan tare da sa aya, ba tare da ka yi 'space' a tsakaninsu ba.
A.M. Ahmad ✅
AM Ahmad ❌
A gujewa amfani da sunaye barkatai, da inkiya (nickname) maras ma'ana, irinsu Itz K-Boy, Princess... Ko amfani da special characters misali, ᾰℓḙḙ⑂ṳ Պ. ᾰℏՊᾰᖱ, ĂĹÊÊŶŨ M. ĂĤMĂĎ, ko ɓoye suna tare da amfani da sunan da ba a sanka da shi ba.
Ba laifi ba ne ka yi amfani da pen name, ko sunanka da sunan gari, mis. Anas Darazo (garin Darazo, Bauchi), ko nisbah, mis.Garba Al-Hadejawy (bahadeje), ko nasaba (patronym) ko alkunya (teknonymy) mis. Bin Sa'eed Abou Salman, ko laƙabi/inkiya (nickname) mai ma'ana, Na Ƴar Talla. Amma kar ka ƙirƙirawa kanka inkiyar da ba a sanka da ita ba. Idan profile naka na kasuwa ne, za ka iya amfani sunan brand, misali Matukin Adaidaita Sahu (sana'ar ce ƙudurinka).
-------------------------------------------
* Bayan sanya sunan inkiya, za ka iya ƙara cikekken suna, ko fullname da nickname; ta hanyar 𝗦𝗲𝘁𝘁𝗶𝗻𝗴 > 𝗣𝗿𝗼𝗳𝗶𝗹𝗲 𝗦𝗲𝘁𝘁𝗶𝗻𝗴 > 𝗡𝗮𝗺𝗲 > 𝗔𝗱𝗱 𝗡𝗶𝗰𝗸𝗻𝗮𝗺𝗲.
-------------------------------------------
A wajen sanya sunan gari, wurin da kake rayuwa ko wurin aiki, ka sa inda kake na haƙiƙa, ko ka bari baki ɗaya. Kar ka sa, a misali, works at STUDENT OF THE YEAR. Ko, kana zaune a 𝗛𝗮𝗱𝗲𝗷𝗶𝗮, ka sa lives in 𝗔𝗯𝘂𝗷𝗮. Ko, kana karatu a Nijeriya, amma ka sa 𝗛𝗮𝗿𝘃𝗮𝗿𝗱 𝗨𝗻𝗶𝘃𝗲𝗿𝘀𝗶𝘁𝘆
Profile ɗinka na da muhimmanci a rayuwarka sosai, ka sa abin da yake na gaskiya, ko ka bari baki ɗaya, shi ya fi. Har pages da kake followings, rubutu da kake, comments da likes a wasu postings, irin abokan da ke friendlist naka duk suna bayar da bayanai game da kai.
• Rubutu mai alaka 👉 bit.ly/3A542OD
✍️Aliyu M. Ahmad
19th Muharram, 1444AH
17th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani
0 Comments