Digiri


Ilimi kalmar Larabci ce (العلم) dake nufin ‘sani’ ko ‘episteme’, sanin haƙiƙanin abu, ɗabi’arsa da kuma alaƙarsa da rayuwa daga "al-‘aql al-hayulani" zuwa "al-‘aql al-fa‘il" (Ibn Sinah cikin دانشنامه علایی). Ilimi shi ne kishiyar jahilci (rashin sani). Ilimi shi ne abin da ke bambanta ɗan Adam da dabba, shi ne kyautar da Ubangiji Ya bawa ɗan Adam na gane abubuwan dake kewaye da shi daga ji, gani, da tunani (Al-Nahl 16:78), karatu (ilimi) shi ne abu na farkon wahayi ga Annabi ﷺ (Alaq 96:1), a cikin hadisi, nemansa aka ce wajibi ne akan dukkan Musulmai (Ibn Majah, 224), ko a wajen Ubangiji masu ilimi daban suke da jahilai (Zumar 39:8 & Mujadala 58:11).

Ilimi abu ɗaya ne, mai tushe da rassa daban-daban. Tarihin tushen ilimi ya kasu daban-daban, misali, daga fuskar addini, Allah Shi ne ya kimtsawa ɗan Adam ilimi, tun lokacin da Ya umarci mala’iku su yi wa Annabi Adamu sujjada “واعلم ءادم الأسماء كلها” (Baqara 2:31), daga nan ɗan Adam yake ƙoƙarin fahimtar abubuwan da suke kewaye da shi, ɗabi’arsu da yadda zai more rayuwarsa da su, yana bauta, noma, sufuri, mu’amala, jagoranci, hukunci, kasuwanci da tattali, jinya, tsaro, tunani… dukkansu akwai fannoninsu a ilmance don inganta rayuwa. Akwai sauran nazariyyat (theories) na asalin ilimi.

A makarantu (academic fields) ilimi yana kasuwa zuwa Humanities, Social Sciences, Sciences da sauransu. A cikin rassan, wasu na alaƙa da wasu (inter-disciplinary mis. Philosophy, ko multidisciplinary, mis. Medicine, ko cross-disciplinary, mis. Language of Engineering). 

Idan muna maganar ‘digiri’ muna maganar matakin karatu (neman ilimi) ne bisa tsarin UNESCO na ISCED, a Nigeria daga 1842 zuwa yau. A digirin nan akwai sashen ilimai daban-daban na ɓangarorin kimiyya, fasaha, zamantakewa da halayyar ɗan Adam. 

Ka kan ji wasu na kushe karatun wasu saboda a tunaninsu in ka kammala karatu ba za ka sami kyakkyawan aikin da kwalin digirinka ba. To wai dama ana karatun digiri ne don a samu aikin gwamnati? Ko dama manufar karatu ana yi ne don samun saƙafar (wayewa ta) zaman duniya da daidaita tunani? Eh! Don dukkan biyun. Amma duk mai tunanin karatu don aikin gwamnati ne (kaɗai) haƙiƙa ya ragewa ilimi daraja da kaso mai yawa kuma ya taƙaita tunaninsa.

Wani zai ce, idan kana buƙatar neman ilimi a ƙarni na 21 ka nemi ilimin fasahar sadarwar zamani (ICT), wani kuma zai ce ilimin kimiyyar likitanci, wannan duk tunanin masu karatu ne don neman aiki, shi kuma karatu ya wuce nan, babu ilimin jefarwa, a kowacce al’umma, a kowanne lokaci, don haka ka daina jin cewa abin da kake karanta wa ba shi da muhimmanci. 

Karatu a makarantun gaba da sakandire (higher institutions), kaso 30% ne karatu, sauran 70% yana cikin saita tunani, mu’amala, gogewar rayuwa, fasahar warware matsaloli [problem solving skills] (shi ya sa ake bada project). Idan ka kammala akwai 57% na yiwuwar ka samu aiki da karatun da ka yi. Ba wa Certificafe muhimmanci ya sa, aka maida hankali kan neman certificate, kawai a yi 'pass', a karbi cert a shiga 'labour market'. Wani har ya gama ba zai iya cikakken bayanin me yake karanta ba.

Akwai kuma rukunin courses da ake cewa ‘marketable courses’, fannoni da ake bukatarsu a lokacin, kamar a yau, ɓangarorin kimiyyar lafiya (mis. Medicine, Pharmacy), fasahar zamani (ICT), gine-gine (Architecture, Engineering…), kasuwanci… ‘Marketability’ na karatu yana dangantaka da zamani ko wuri, misali a 1900s aikin ‘malinta’ aka fi bukata a Nijeriya saboda karantar da mutane 3Rs (karatu, rubutu da lissafi), daga baya aka ɗaukaki ABC (Army, Banker da Customs).

A wannan ƙarnin, a wannan ƙasa (Nijeriya), ya kamata mu fara sake tunani, daga karatu-aiki, zuwa karatu-dogaro-da-kai. Don ka karanci Education ba ya nufin sai ka sami aikin koyarwa, haka Linguistics, ko Basic Sciences. Political Science ba ya nufin ka fito takarar siyasa ba ne, a’a, mai sharhi da bincike kan al’amuran siyasa dai, kamar yadda Literary Critics ke duba adabi, ko Public Admin ka ce sai ka sami aikin office… an wuce irin wannan tun 1900s lokacin da ake neman ma’aikata ruwa a jallo, yanzu civil services ya yi wahala. Ilimin zai ma amfani wajen gina tunaninka ne na rayuwar duniya. 

Misali, Kwankwaso, Water Engineering ya karanta, amma ga shi yana siyasa, saboda yana da SQ (Social quotient). Elon Musk ‘Economics’ da ‘Physics’ ya karanta, amma yana jagorantar duniyar bincike a sararin samaniyya (SpaceX). Jack Ma mai Alibaba, English ya karanta, da ya yi aikin koyarwa, daga baya zama babban ɗan kasuwa. Asali ma, Steves Jobs na iPhone da Mark Zuckerberg na Facebook, Michael Dell, Evan Williams na HP, Twitter da Medium, Larry Ellison na Oracle, Jan Koum na Whatsapp, dukkansu dropouts ne,  ba su dogara da kwali ba.

Idan kana maganar sai da kwali za ka rayu, ka yi aiki, akwai abokina da muka yi legal, shi Qur’anic Science ya karanta (Diploma) amma yanzu yana aiki a CBN. Akwai kuma wanda yake da First Class a Accounting, a lokacin da bankin da suka ɗauke shi aiki suka zo rage ma’aikata, har da sunansa aka rage, amma aka bar abokinsa mai Third Class a Biology ya ci gaba da aiki.

Kamar ni, a 2009 na zana jarrabawar Science and Technical, Allah bai ƙaddara na je ba. Na sa a raina ina son aikin jarida, na yi JAMB 2012, Mass Communication, ABU Zaria, har POST-UTME na yi da score 198, shi ma Allah bai ƙaddara zan yi karatu a Zaria ba. 2013 na shiga JSCILS na karanci Civil Law, bayan na kamala na yi burin tafiya LLB, shi kuma sai da Literature a O’Level. Na yi private WAEC, NABTEB da School WAEC tsakanin 2016-2017 ina neman literature, kuma na samu, na cike D.E. Law a Bauchi State University (Misau Campus), ban samu ba, sai na samu English and Literary Studies a BASUG ɗin dai. Ban shiga ajin ‘science’ ba, ban karanci Physics ba, amma a tsakanin 2017-2018 lokacin ina karatun Philosophy, Isah Abubakar nake zuwa ina ɗaukar karatun Quantum Physics da Special Relativity, saboda akwai buƙatarsa. Ina karatu, ina aiki Computer Graphic Design. Kuma karatun addini, law, linguistics, literature, philosophy, physics da IT sune suka daidaita tunani da nake a yanzu, duk da akwai ƙalubalen rayuwa.  

•  Ka daina jin kana karatu don neman aiki, ka yi karatu, ka riƙe sana’a, idan Allah Ya kawo aikin sai ka karɓa. A yau, ko aiki za a ɗauka, sun fi son mai ‘experience’ na wata mu’amala.

•  Ka daina jin wani yana karatu da ya fi naka, dukkan karatu ana yinsa don inganta rayuwa ne; wataƙila ta silar naka ka fi shi nasibin rayuwa. 

•  Ka daina kallo ma wani ƙasƙanci, don yana karanta wani fanni da kake wa kallo yana ƙasa da naka; wanda ya san darajar ilimi, ya san babu ilimin da yake na yasarwa.

•  Ka yi tunani fiye da kwalinka. Kowanne fanni kake karanta, ka yi kokari yi da gaske, ta iyu karatun da ka yi daban, baiwarka badan, ka gano baiwarka, sai ka gina kanka a kan wannan. 

✍️ Aliyu M. Ahmad
17th Muharram, 1443AH
15th August, 2022

#AliyuMAhmad 
#RayuwaDaNazari
#Digiri

Post a Comment

0 Comments