Matsalolinmu


Matsalolin da muke ciki a ƙasarnar fa, sun girma a tattauna su a teburin mai shayi, majalissar da ba a warware matsala, sai dai (a yi ta) musu da jayayya. Ina son yin magana, amma kar ku min kallo ta fuskar siyasa.

Bayan matsalar tsaro, taɓarɓarewar ilimi, karyewar ₦aira da hauhawar farashi... shekara mai zuwa za a sami ƙarancin abin ci, ƙaranci kuma na nufin wanda yake ajiye zai yi tsada (p=f(x)) saboda dalilin yaƙin Russia da Ukraine, ga kuma wasu yankuna a Arewancin Nijeriya da ba a noma (saboda bandits), ga ambaliyyar ruwan sama (sai dai Allah Ya kiyaye).

A yau ko albashi kake ɗauka, kuɗin cefane (na wata), ya ninka, babu abun da kuɗinsa bai ƙaru ba a kasuwa. Gidaje da yawa da a kullum suke miya da kifi ko nama, an janye wannan. Masu shan madara, su ci kwai a breakfast ma yana nema ya gagara. Abin da mutane da yawa suke fafutuka a yanzu shi ne abin da za a ci a rayu, da daɗi ko ba daɗi. Ga jagorori ko a jikinsu.

Maimakon mu tsaya muna ƙorafi (ƙorafin da ba zai kawo mana mafita ba), mu sake neman hanyoyin neman rufawa kai asiri (kuɗi). Ya zame mana wajibi, mu taƙaita kashe kuɗade kan abubuwan da ba dole ba, mu yi ta abin ci, idan za ka iya siyan abincin shekara ma, ka siya ka ajiye. Mu yi koyi da darasin aya ta 43 - 49 ta cikin Suratu Yusuf.

'Ya'ya ku jinjinawa iyayenku, matan gida, ku jinjinawa mazajenku masu fafutukar rufa muku asiri. Gaskiya mu sanya duniya a cikin addua, Allah Ya iya mana, Allah Ya kawo mana sauƙi.

✍️Aliyu M. Ahmad
21st Muharram, 1444AH
19th August, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments