Alamy

#WorldPhotographyDay

Hotuna da muke ɗauka yau da gobe fa kadara ce, domin akwai shafukan da in muka ɗora su za su (iya) saye, a biya mu da dollar $💵 (i.e. stock photography)

Kamar manhajar Alamy.com, bayan ka yi rijista, ka sami lasisi, idan ka ɗora hoto a wannan shafin, aka sami mai saye (buyer/client), idan wanda ya saya zai haɗa flier ta talla, zai biya $500, idan a cover ta littafi za a yi amfani da shi, za a biya ka $150, idan kuma a online (kamar website, social media…) za a yi amfani da hoton da ka ɗauka ka ɗora a Alamy, za a biya ka $20.

* Za ku iya sauke shi a Playstore 👉 bit.ly/3CgjTN9 iPhone/iSO 👉 apple.co/3T4xXz1 (Stockimo) ko (kuma) ta shafinsu alamy.com don yin rijista.

Da kyawawan hotuna da muke ɗorawa a Instagram ko Facebook, ka nemi yadda za kana freelancing, ko maida kanka BRAND AMBASSADOR, ana amfani da hotunanka wajen tallace-tallace, ana biyanka. 

Akwai suran shafuka da ake ɗora zane-zane da hotuna na jeji, ruwa, gine-gine ake siyarwa a sami kuɗi irinsu su Shopify, Amazon, iStock, Pinterest, Pixlr, Flickr, Deposit Photos, Pexels, 500px, Shutter Stock, Getty Images, Dreams Times, 123rf, Snapwire, Foap, Vista Create,... da sauransu. Sa zarar ka shiga Creator Rewards program, hotunanka za su zama kuɗi.

--------------------------------------
• Rubutu mai alaka 👉 bit.ly/3pxPv9o
--------------------------------------

✍️Aliyu M. Ahmad
21st Muharram, 1444AH
19th August, 2022CE

#AliyuMAhmad
#FasaharZamani
#WorldPhotographyDay

Post a Comment

0 Comments