Marka Marka II


Akwai waÉ—anda da za a yi sati ko wata ana wannan ruwan, ba za su fito waje ba, ba su da damuwa, domin Allah Ya hore musu abin da za a ci, kuma suna zaune cikin gini mai aminci. Wasu kuwa, ko da ruwan rabin yini aka yi, sai sun jigata, sun tagayyara, daÉ—inta kawai, don ba a zafi ne, a yanayin akwai sanyi.

Ina zaune na tuna, ashe akwai gidajen da suke abin cin siyarwa, kuma sai an ɗauka a fita da shi bakin kasuwa, ko kofar tasha ko bakin titi, tukun a siyar, ribar a rufawa gida asiri na 'yan buƙatun yau da kullum. Amma jiya, akwai waɗanda sun yi asarar abin da suka dafa na siyarwa, saboda ruwa, babu halin fita, kuma ya fi ƙarfin a cinye dukka a gida.

Ta wani ɓangaren kuma, akwai masu iyalin da sai sun fita tukun su nemo abin da za a ci a ranar, ruwa ya hana su ita jiya, yau ma ta masu ƙarfin hali ce, ba yadda za a yi ne.

Kawai sai na yi tunanin, JIFAR TSUNTSU 2 DA DUTSI DAYA. Idan da za tallafawa mutanen nan, sai ka sayi abin ci waÉ—ancan, ka bawa waÉ—annan, a lokaci guda, duk ka taimake su. Ko kuma, ka duba waÉ—anda suke halin tattare kayansu, ko kwashe ruwan da ya cika musu gida, su ma waÉ—annan ba su da sukunin É—afa abin ci, ana ta muhalli.

اللهم سقيا رحمة، ولا سقيا عذاب، ولا بلاء، ولا هدم، ولا غرق، الّلهم على الظّراب، ومنابت الشجر، اللهم حوالينا ولا علينا 🤲

✍️ Aliyu M. Ahmad
5th Muharram, 1444AH
3rd August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyuCares

Post a Comment

0 Comments