GBWhatsapp




Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana wasu tsaruka (features) da 'Whatsapp' na asali ba shi da su, kamar:

1. Adana (saving) na hoto, bidiyo 💾 daga status, ko kuma
2. Kwafin rubutu daga 'status(es)' na mutane kai tsaye 📄, ko
3. Ɓoye alamar karantawa ko karɓar saƙo (receipt) ☑️, ko
4. Yana nuna alamar in mutum na online 🟢, ko don
5. Tura 'file' mai nauyi📤, ko
6. Ɓoye groups/chats (hide chat) 🧑‍💻, ko
7. Rubuta sunan 'group' da harafai sama da 35 👪,
8. Yin status da harrafai 250; a taƙaice 🤳, ko
9. Auto reply 📱, ko
10. Forwarding message zuwa ga sama da mutum ko groups 5 a lokaci guda ⤴️, ko
11. Amfani da fonts style kala-kala🔡,
12. Ware groups da personal chats daban...

Eh! GB yana da wasu ‘features’ da whatsapp.com ba shi da su...

...amma, ka san ba sahihi ba ne? Mods ne, sun tsara shi ne ta yadda zai baka sha’awa sosai, fiye da manhajar ta asali (normal Whatsapp), tare da baka damar wasan ɓoyo da ma’abota amfani da Whatsapp, musamma ma ƴan uwa mata, ka tura saƙo, a karanta, amma ba zaka ga alamar an karanta ba ✅, sannan a duba status ɗinka ba tare da ga wanda ya gani ba 👀...

Tom! Maganar gaskiya kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne; ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an ƙirƙire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba.

Ina gargaɗar masu amfani da GB, ko son amfani da shi, da su ƙauracewa manhajar saboda (wasu daga cikin) dalilai kamar haka:

• Na farko, GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp. ‘AlexMods’ ne masu amfani da XDA (Xerox Device Agent) suka ƙirƙire shi (ana ƙiransu Has.007). Ba su da lasisi, kuma sun karya ƙa’idar ƙirƙirar da bada lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba zaka sami manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taɓa ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa, babu! Ko a Facebook in ka rubutua GBWHATSAPP ka kara da .com, ka yi posting, za su gargaɗe ka, ko su yi banning na account ɗinka.

• Na biyu, mai amfani da GBWhatsapp, ya yi sani, duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya leƙawa ba, siyarwa, ko amfani da ba shi a duk lokacin da suka dama.

• Na uku, idan aka turo ma wani sako mai ɗauke da ‘virus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa kamar 'spyware' ne, ai kama kana amfani da shi wajen ganin sirrin wasu, ba tare da saninsu ba.

• Na huɗu, duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi yasa, yawanci waɗanda ake musu kutse (hacking) ta Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YO… da sauransu, ko waɗanda ba sa Two-Step Verificafication.

• Na biyar, GBWhatsapp in ya yi 'expire' (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har 'groups' da kake ciki, sai ka nemi a maida ka (re-adding).

• Na shida, ka lura, a duk lokacin da ka ɗauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargaɗeka cewa, wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka; baka taɓa lura ba? In ka taɓa lura da haka, don me zaka sa kanka a halaka?

• Na bakwai, idan don wasan ɓoye kake amfani da GBWhatsapp, tom, normal Whatsapp ma yana da feature ta boye blue stick ☑️ (na karanta chat), ka shiga SETTINGS > ACCOUNT > PRIVACY sai TURN OFF READ RECEIPTS.

👉 Idan kuma don downloading ne, ka yi amfani da XENDER ko PHOENIX BROWSER man, don sauke hoto ko videos na contacts ɗinka.

👉 Idan don ɓoye chats na wani, akwai ARCHIVE, da long press a kan chat, sai ka duba 'option bar' a sama, za ka ga 'archive icon' 📥, sai archiving.

👉Idan don 'auto reply ne' WHATSAPP FOR BUSINESS yana yi, Android (bit.ly/3AXc8Ld), iPhone/iSO (apple.co/3ROgRov).

👉 Idan don status text copy ne, masu wayoyin iPhone da Samsung Photos, suna iya copying text daga screenshot. Ko kuma, ka yi amfani da Google Lens, Android (bit.ly/3OTF8qD).

👉 Idan don tura file mai nauyi ne, ko video, zai attaching sa 'as document' 📄.

👉 Akwai Whatsapp guda 3 kadai suke sahihai:

1. Whatsapp Messenger (normal/personal)
• Android: bit.ly/3JzNJOb
• iSO/Apple: apple.co/3BF882g

2. Business Whatsapp
• Android: bit.ly/3AXc8Ld
• iSO/Apple: apple.co/3ROgRov

3. Whatsapp for Web (PC/MAC):
bit.ly/3zs6LkZ

Kar ku yaudaru! GBWhatsapp 'mods' ne, zai iya cutar da kai yau ko gobe. Kuma a kowanne lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da manhajar (banning).

✍️ Aliyu M. Ahmad
19th Safar, 1443AH
27th September, 2021CE

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #GBWhatsapp #Whatsapp #BeCyberSmart #Privacy

Post a Comment

0 Comments