Rangwame

 

#Rangwame

Tabbas! An ce Gwamnatin Nijeriya za ta ƙara kuɗin data da kuɗin ƙiran waya (bit.ly/3p3lWMv). Yanzu abin da ya kamace mu shi ne neman hanyoyin samawa kanmu sauƙi da rangwame, tunda amfani da data da kuma ƙiran waya suna daga cikin 'necessities' na tafikar da rayuwar yau da kullum, musamma a kasuwancinmu.

Ban san wa wannan zai taimaka, amma ni na jima ina 'yan wasu dabaru don samawa kaina sauƙi, tare da more tsare-tsaren gidan waya (na MTN).

A wata (monthly), na kan sa 50GB a tsarin MTN Data4Me (*121#) a kan kuɗi ₦6,000, tun March, 2021. Da suna ban 20GB a ₦3,500 da 40GB a ₦5,000, daga baya ne suka upgrading layina zuwa 50GB, 80GB da 150GB.

Da na yi nazari, haka kurum duk wata zan riƙa sawa waya ₦6k na data (kurum), kuma bayan haka akwai kuɗin ƙira da zan riƙa sawa akai-akai. Na yi nazari, na ce ya kamata na nemowa kaina wani rangwame.

Na duba cikin tsarukan MTN (Tariff Plan), sai na ga tsarin BETATALK su kan bada 300% bonus na kowanne recharging da ka sa a waya. Idan ka ₦100, za a baka bonus na ₦300 (300%), kuma wancan ₦100 taka tana nan.

--------------------------------------
Yadda ake komawa MTN BetaTalk:
• Ka tura 'BT' zuwa 131 (ta SMS)
• Ko ka latsa *123*2*1#
--------------------------------------

Ka ga, idan na sa ₦6,000 za a ba ni ₦18,000 (kuɗin ƙiran waya), kuma wancan ₦6000 tawa tana nan (dat ita zan yi subs). Zan yi subscription na data 50GB Monthly, kuma ina da ₦18,000 na ƙiran waya, na tsawon sati guda.

Wannan ₦18,000 ta BetaTalk bonus, ana jan 73k/sec (N43.80/min), gaba ɗaya 410 minutes (6 hours) kenan, a sati.

Bayan sati, idan Bonus na ₦18k ya ƙare, ko wa'adinsa ya cika, ba za iya ci gaba amfani da BetalTalk a kan tsarin biyan 32.50k/sec (a kan airtime nawa), da kuma 73k/sec (na bonus) ba. Saboda haka, sai na koma MTN Pulse da ake biyan 11.26k/sec na ƙira, da 'Nightlife Data.'

A tsarin MTN, in za ka koma wani tsari (Tariff Plan) sai ka biya migration fee na ₦102 idan ka canja tsari cikin ƙasa da wata 1, AMMA NI BA NA BIYA. Yadda nake yi shi ne, zan sayi 'Nightlife Data' ta ₦25 (250MB) da *406*3*1*1*1# kai tsaye, za su ban 250MB. MTN za su maida ni tsarin Pulse ba tare na biya migration fee ba.

Idan kuma datar ta ƙare kafin ƙarshen wata, na kan amfani da MyMTN app don siyan data. Siyan data da MyMTN na da rangwame sosai. Misali, ta *131*1# ana siyar da ta 2GB a ₦500, amma ta 'app' 2.5GB za a baka a ₦500.

---------------------------
MyMTN App: Android (bit.ly/3QaXc0N), iPhone/iSO (apple.co/3Qzrnii).
---------------------------

Idan kuma ba ni da recharge card a waya, yawancin mutanen da nake mu'amala da su, mu kan yi 'voice call' ta Whatsapp, Telegram ko Facebook Messenger da data.

-----------------------------------------
Rubutu mai alaƙa da rangwame 👉 bit.ly/3QMHRUn
-----------------------------------------

✍️ Aliyu M. Ahmad
11th Muharram, 1444AH
9th August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Rangwame #VoiceCall #MTNPulse #BetaTalk

Post a Comment

0 Comments