Matakan Ruguza Rayuwa



 Matakan farko da za ka bi don ka faɗi warwas a rayuwar nan, su ne, ka ce (kai) sai ka 👇


1. Kwaikwayon rayuwar wani, ko 

2. Yin gasa da nasarar wani, ko 

3. Yin komai don burge mutane, ko neman yardarsu.

4. Girman kai, jiji da kai da raina mutane.

5. Lalaci da kasala.


Allah Ya halicce mu mutane daban-daban, kowa da gwargwadon baiwarsa, kowa da gwargwadon arzikinsa. Idan ka sa a ranka sai ka yi rayuwa irin yadda wani (da ya fi ka) yake, sai ka mance da baiwarka da kason arziki da Ubangiji Ya tsaga ma, kuma ba za ka yi nasara ba, saboda ka yi shifting, from ORIGINAL to PHOTOCOPY.


Don abokinka ya mallaki wani abun duniya, kamar wayar hannu, ko sutura, ko  abin hawa, ko muhalli, ko aure... kafin ka fara tunanin yin gasa da shi, ka fara tunanin hanyoyin samu irin nasa. Ta iyu ma kuna samun kuɗi iri ɗaya, amma nauye-nauyen rayuwarku ba iri ɗaya ba. Da wannan sinadarin na gasa cutar HASSADA ke shiga wa mutum. Ana yin gasa da rige-rigen aikin alheri, ko rige-rigen neman ilimi waɗannan halastattu ne, daga Ibn Umar da Ibn Mas'ud رضي الله عنهما, daga Manzon Allah ﷺ (Fath-al Bari 1/177).


Idan kuma kana tunanin yin rayuwa don burge mutane ne, ka sani, da yawa cikin waɗanda kake son burgewar ma, haushi kake ba su (ɗan mai iya yi). Kar ka matsawa kanka yin abu don farantawa mutum, ka kuntatawa kanka. Duk wani aiki da za ka aikata don neman yardar mutane, hatta a wajen Ubangiji ma, ba karɓaɓɓe ba ne. Duk wani abu da za ka mallaka don burge mutane, ba ka cancance shi ba, saboda ba kanka ka siyawa abun ba, idon mutane ka siyawa.


Girman kai kuma shi ne ƙin karɓar gaskiya da kuma raina mutane. Mai girman kai ba ya taɓa jin yana kuskure, ba ya karɓar kuskure ko gyara, saboda ya raina mutane ba zai koya ba... da zarar mutum ya buɗe wa kansa wannan ƙofar, ya kashe kansa muɗus a fagen neman ilimi ko neman halal.


✍️ Aliyu M. Ahmad 

6th Muharram, 1444AH

4th August, 2022CE


#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments