STOP PROCRASTINATING: A SIMPLE GUIDE TO HACKING LAZINESS, BUILDING SELF DISCIPLINE, AND OVERCOMING PROCRASTINATION
• Mawallafi: Nils Salzgeber
• Yare: Turanci/Ingilishi (English)
• Shafuka: 116
________________________
#Jinkirtawa!
Rayuwar yau, ta fi ta baya sauki, amma mutanen yau, sun fi na da lalaci da jinkirta aiyukan gabansu masu muhimmanci.
A misali, mutanen yau mun sami sauki da wayar hannunmu, ta maye ma guraben abubuwa da yawa: agogo, talabijin, recorder, camera, wasanni, kalkuleta, littafi, kwanfuta, kyallamara, fos... Muna zaune za muna iya gudanar da wasu aiyukan. Misali, a da in kana son siyo a daga wani waje/gari, ko isar da wani sako, sai ka hau mota ka je, amma yau waya ko order a yi ma waybill.
Duk da samun wannan saukin, amma muna yini mu kasa cika wani aiki da muka yi niyyar yi cikin yini mai muhimmanci, har muna mamaki YAU TA WUCE BAN YI KAZA-DA-KAZA ba, MUNA TA KARYAR BUSY, BUSY... me ya sa?
Wannan littafin zai taimaka ma sosai wajen shawo kan wannan matsalar.
_________________________
Za ku iya sauƙe shi (PDF) ta wannan link dake kasa 👇
DOWNLOADING• Nauyi (size): 1.4MB
Allah Ya amfana.
✍️ Aliyu M. Ahmad
23rd Dhul-Hijjah, 1443AH
22nd July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Karatu #GyaranTunani #AliyusLibrary #ReadingCulture #Procrastination #WeekendReading
0 Comments