Littafin Ahlari




Littafin Ahlari, ko Matn Alkhdari  (كتاب متن الأخضري في العبادات على مذهب الإمام مالك), Imam Abu Yazid Abdurrahman bin Muhammad Al-Akhdary (918AH – 983AH) ne ya rubuta shi. 


Littafi ne sananne a fiqhun Malikiyya  da yake bayani kan ibada. Kuma shi ne littafi a matakin farko ga almajiran Fiqhun Malikiyya, kafin karatun Fiqhul Muqaran, Usulul Fiqhi, Qawa'idul Fiqhiyya da Maqasid.


Bayan kammala karatun AHLARI, a mafi yawan wurare, bi sa al’ada, xalibin zai xora da littafin Al-Ishmawi, Al-Iziyya, Risala ta ibn Abi Zaid… har zuwa Mukhtasar na Khalil, Mudawwamanah ta Sahnu, Shuruh na Muwatta da sauran manyan littattafan fiqhun Malikiyya. 


An ce, Imamul Al-Akhdari ya rasu 983AH kafin ya kammala rubuta littafin, saboda a niyyarsa, ya so ya rubuta littafin Fiqhun Malikiyya ne da ya shafi ibada da mu’amala baki xaya, sai Allah Ya kar vi rayuwarsa a daidai lokacin da ya zo “إِلاَّ أَنْ يَكْثُرَ النَّاسُ خَلْفَهُ فَيَتْرُكَ يَقِينَهُ وَيَرْجِعَ إِلَيْهِمْ” na fasalin Rafkanuwa na littafin. 


Dalilin ya sa ake bawa xalibin ilimi shawarar farawa da Ahlari kafin kinkimo manyan littattafan fiqhu, ko na fiqhun wata mazhabar, shi ne, BAI YIWA YARA GIRMA BA, BAI KUMA YIWA MANYA QANQANTA BA. Littafin na Ahlari yana da bayanin yadda mutum ya kamata ya kasance a matsayinsa na Musulmi a ibada, halayya da mu’amala tsakanisa da sauran mutane. Littafin ya yi  bayanin tsarki da sallah (ibada da ake yau-da-kullum), ga mas’alar rafknuwa (sahwu) da aka yi bayaninta dalla-dalla cikin littafin fiye da litattafan da suke gabansa (Al-Ishmawy da Al-Iziyyah). A ko’ina kake, idan ka samu malamin da zai iya karantar da kai sosai, tare da bayani filla-filla, za ka fahimci ibadar tsarki da sallah sosai. 


Saboda ci gaban zamani, akwai malaman da suka karantar da shi aka xora a yanar gizo (internet), ta yadda za ka iya sau qewa karatuttukan a wayarka, kana bi, ko kana saurara:


• Dr. Jabir Maihula bit.ly/AkhadriDrJabir

• Dr. Jamilu Zarewa bit.ly/AkhadarDrJamilu

• Dr. Zubairu Madaki bit.ly/AkhadariDrZubairu

• Sheikh Abubakar bit.ly/AkhadariSAbubakar

• Sheikh Khamis Almisry bit.ly/AkhadariKhamisMisry


Akwai kuma fassarar littafin da Hausa a kasuwannin littafai na Mal. Abubakar Muhammad Tsangarwa, ko kuma mai fassara da sharhi na Dr. Jamilu Zarewa.


• Akwai PDF (Arabic) bit.ly/3aQrjv5

• Akwai PDF (English) na Ibrahim Saidy bit.ly/3Pp7xpx 

da na Muhammad Rami Nsour Al-Idrisi     bit.ly/3PGhBu1 


Akwai Fassarar Ahlari na Hausa na “Android” a Google Playstore: 


• Maftal Amfay  bit.ly/3zkKuqo

• Abubakar S. Salihu  bit.ly/3Bl9CyT


“Duk wanda Allah Ya nufe shi da alheri, sai ya sanar da shi addini” [Sahih Muslim, 1037]. 


Allah Ya datar da mu.



✍️Aliyu M. Ahmad

21st Dhul-Hijjah, 1443AH


20th July, 2022CE




#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Ahlari #AliyusLibray #Karatu #LattafinDonGyaranIbada

Post a Comment

0 Comments