Bincike Cikin Waya

 



Idan kuna buƙatar kwanciyar hankali da zama mai ɗorewa tsakaninku da abokan zamanku, ku guji bincike cikin wayoyin junanku, saurayi da budurwa ko mata da miji.

IN DAI DA SO, TO DA YARDA! Matuƙar za ka yi soyayya ko zaman aure da mutum, dole akwai aminci da yarda. Domin da zarar zargi ya fara gilmawa tsakanin abokan zama guda 2, komai sai ya dagule.

Wani lokacin, alheri ne rashin sanin wasu sirrikan abokan zama, domin da zarar ka san wani, za ka shiga cikin tashin hankali, damuwa da rashin samun nutsuwa.

Babu amfanin mu'amala kowacce iri da mutum da baka yarda da shi ba, ko mai yawan zargi a kanka, matuƙar ba fili ta fito ba.

Idan ɗayanku ya ci amanar ɗaya ma, SHI YA SO, kuma duk daren daɗewa, za ta fashe, ba sai kuna binciken abin da zai tada muku hankali ba. WANDA YA CI AMANA, AMANA ZA TA CI SHI/TA.

✍️ Aliyu M. Ahmad
27th Dhul-Hijjah, 1443AH
26th July, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments