Littafi domin #GyaranTunani (4)




THE POWER OF FOCUS: HOW TO HIT YOUR BUSINESS, PERSONAL AND FINANCIAL TARGETS WITH ABSOLUTE CONFIDENCE AND CERTAINTY

• Mawallafa: Jack Canfield, Mark Hansen & Les Hewitt
• Yare: Turanci/Ingilishi (English)
• Shafuka: 361
________________________

MAIDA HANKALI (FOCUS)

Duk abin da ka a gaba matuƙar za ka maida hankali kuma ka bi matakan yi/samu, haƙiƙa za ka za ka yi nasara.

Ijtihadi (himma) da mayar da hankali (focus) su ne abubuwan da suka bambanta nasarar mutanen da (iyayenmu da kakaninmu), da mutanen yau (mu) a neman ilimi, dukiya, ɗaukaka, aiki...

Ƙaramin misali:

Idan ka bi tarihin ƙaramar sana'a ake a gidanku (mahaifinka), za ka ga, da ita aka gina muku gida, aka haife ku, aka raine ku, kuma har yau ake riƙe da gida da ita... Amma yau kai a naka tunanin ta ma kaɗan, da za a tattare ma jarin, bai fi ka sayi sabuwar waya da sabuwar shadda ba.

Me ya sa?

Ka karanta wannan littafin POWER OF FOCUS, haƙiƙa tunaninka zai sauya a al'amuran rayuwa da dama.
_________________________

Za ku iya sauƙe shi (PDF) ta wannan link dake kasa 👇

bit.ly/3OIpgHv

• Nauyi (size): 5.61 MB

Allah Ya amfana.

✍️ Aliyu M. Ahmad
30th Dhul-Hijjah, 1443AH
29th July, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Karatu #GyaranTunani #AliyusLibrary #ReadingCulture #Focus

Post a Comment

0 Comments