Influencer
shi ne mutumin da ake amfani da iliminsa ko baiwarsa kan wani ilimi ko
kwarewa, tare da ƙoƙarin bayyawa duniya hakan a cikin posting da yake yi
a social media (Geyner, 2022).
Influecing
a Hausance, za mu iya fassara ta da TASIRI, ma'ana, a duk yayin da
Influencer ya yi rubutu, wannan wallafar zata yi tasiri a wajen masu
bibiyar shi (followers).
Influencers
a social media sun kasu kashi-kashi, akwai MEGA-INFLUENCERS, wanda yake
da followers sama da miliyan (1m+), irin waɗannan su ake ƙira da
CELEBRITIES, yawacinsu jarumai ne a masana'antar fina-finai, mawaƙa, ko
'yan wasa kwallo, ko 'yan siyasa... kamar Ali Nuhu Mohammed (film), Ahmed Musa (kwallo) da Shugaba Muhammadu Buhari da sauransu.
Akwai
MACRO-INFLUENCERS, sune masu followers 40k - 1million. Waɗannan an fi
samun su a cikin rukunin B-Grade, ma'ana 'yan film ko mawaƙa masu
tasowa, ko wasu masana a wani fannin, ko masu aiyukan jinƙai, ko ƴan
kasuwa... misali Fauziyya D. Sulaiman (aikin jin kai), Jafar Jafar (dan
jarida), Uwa Aishatu Gidado Idris (zamantakewa), Dr. Aliyu U. Tilde (siyasa, ilimi da zamantakewa), Beelalgy (sutura da rayuwar hutu)... da
sauransu.
Akwai kuma
rukunin MICRO-INFLUENCERS, sune masu followers 1k - 40k. Yawancinsu
marubuta ne kan wasu fannonin ilimi da mutane ke amfana. Misali,
Badamasi Aliyu Abdullahi (kasuwanci), Mohiddeen Ahmad (fasahar sadarwa),
Anas Dazaro (Motivational speaking), Ibrahim Y. Yusuf (harkokin
lafiya), Abdulrazak Rogo (technopreneur) ... da sauransu.
Akwai
kuma rukunin NANO-INFLUENCERS, sune masu followers kasa da 1k, amma
suna bada gudunmawa sosai a media, sai dai ba su da followers da yawa,
misali Sheikhul Hubb (kan halayya)... Ibn Magaji Alhausawi (Nahwun
Hausa), Ukasha Ismail (tsaro)... da sauransu.
Akwai
kuma rukunin FAKE-INFLUENCERS, za a iya samun irin waɗannan a kowanne
rukuni na sama, sai dai kashhhh! Ba su ne mutane na asali da suke amfani
da shafin ba, sun yi satar suna ne, domin samun followers, kamar Zahra Mansur (Musa L Maje), da sauran masu amfani da sunan mata, ko amfani da
sunan wasu shaharru wajen wallafa barkwanci da sauransu. KO kuma masu
amfani da wani tsari ko manhaja (apps) da take ƙara yawan 'followers' da
'reactions' a social media.
AMFANIN INFLUENCER A SOCIAL MEDIA
1. TALLACE-TALLACE
Idan
ka shiga Kano zaka ga tallar Popcola tare da hoton Ahmad Musa, ko Ceakers Custard tare da Ali Nuhu Mohammed... ana biyan irin waɗannan
INFLUENCERS ɗin miliyoyin kuɗaɗe domin yin tallace-tallace wa kamfofani,
waɗannan rukunin ana ƙiransu da PERSONAL BRAND, ma'ana, sun zama
ambassadors (jakadu) ga waɗancan kamfanoni, domin yi musu
tallace-tallace.
2. TASIRI GA TUNANI
Mutane
irinsu Farooq Kperogi da Na Ƴar Talla, suna da matuƙar tasiri wajen
juya tunanin mutane, a siyasa, ko tsarin zamantakewa. Ana ƙiran irin
waɗannan da OPINION LEADERS, saboda mutane ne da suke da masu bin ra'ayinsu da yawa (cikin (followers), ko sawa mutane shakku da zarar sun yi wallafa.
3. AIYUKA DA NGOs
Akwai
mutane da dama da suke aiyukan wayar da kan jama'a ta sanadiyya
Influencing a Social Media tare da wasu ƙungiyoyi (NGOs) ko samun damar
zuwa (wasu) manyan taruka (conferences). Misali Ismail Auwal, Aliyu Dahiru
Aliyu, Misbahu El-Hamza, Salim Yunusa, Aliyu Samba da sauran.
4. BUNƘASA KASUWANCI
Wasu
na iya amfani da 'influencing' da suke da shi wajen bunƙasa
kasuwancinsu sosai. Misali Anas Darazo (hula), Mallam Garba Al-Hadejawy
(maganin gargajiya), Aminu Muhammad Danliman (kayan sawa/textiles),
Maryam Gatawa (kayan yaji/spices)... da sauransu.
5. TALLATA 'YAN SIYASA
Tara
followers ya sa Rabiu Biyora da Datti Assalafiy amfanuwa da siyasa, har
suke samun kwangilar tallata wasu 'yan takara (aspirants/candidates).
Kar ku yi mamaki don Gwabna Alhaji Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bawa
'yan film muhimmanci, duk yana cikin tsarin 'influencing'.
6. ISARWAR DA GWAMNATI SAƘO
11
ga watan Yuli, 2020 Miladiyya, Salim Yunusa ya yi posting a Twitter kan
lalacewar wata hanya a Banzauzzau, Kwarbai Zaria, cikin amincewar Allah
sakon ya isa ga Gwamnatin Kaduna, ga shi yanzu har an gyara hanyar,
sanadiyyar 'influencing'.
TAMBIHI
1.
A ƙasashen wajen, masu followers da yawa a social platforms, idan
adadin 'followers' ɗin ya kai wani mataki, suna karɓar kwagilar
(contract) daga kamfanoni domin yin talla, kuma a biya su da miliyoyin
kuɗaɗe. Ko yanzu ma a nan Nigeria, ana karbar tallar #MoMoBetterPassCash da sauransu.
2.
Tabbas! Hatta 'yan siyasa na tsoron INFLUENCERS, me yasa? Saboda suna
da yawan followers, maganarsu a media na da tasiri sosai, ta yadda
saƙonsu ke iya kaiwa ga duban mutane cikin ƙanƙanin lokaci.
3. Idan kana influencing a media, ka yi amfani da damarka wajen haɓaka kasuwancinka kowannen iri ne. Ka duba, hatta Nafisat Abdullahi da Rahama Sadau suna tallar kayan kwalliyar mata (cosmetics) a social media, Sada Suleiman Usman ma ambassador ne ga Legend Textiles Ltd. na su Mukhtar Mudi Sipikin. Ga Matukin Adaidaita Sahu (logistics), Abdulhadi Dankama (fruits)... kuma suna samun 'customers' da yawa daga social media. Ga kuma Fadila H Aliyu da Bashir Sani Abubakar dake tallar
#MoMoBetterPassCash na #MTNNigeria.
4.
Kar ka ɗauki influencing da ɗaukakarka a matsayin burge mutane kaɗai,
ko neman suna, BABU RIBA; ka yi amfani da ita wajen gina kanka da
tallafawa yankinka. Kwanaki Bamai Dabuwa ya yi amfani da Facebook wajen
nemawa wasu yara daga yankinsu tallafi zuwa asibiti. Da social media
Comr Abba Sani Pantami da Comr Haidar Hasheem Kano suke amfana da
Jaridar Rariya...
* NEMAN AFUWA
Don
Allah! Duk wanda ya ga na yi mention ɗinsa (cikin INFLUENCERS), ba da
izininsa ba, ina neman afuwa, na yi anfani da sunayen ne a matsayin
misali cikin rubutuna. Allah Ya kara ɗaukaka, da bada kariya, amin.
13th Dhul-Hijjah, 1443AH
12th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani #Hausa #Influencer

0 Comments