1. @ - AT SIGN
Ana amfanin @ (at sign) a social media wajen sauƙaƙa 'mentioning' na mutum a cikin 'posting' ko ƙasan 'comment'.
Misali, wani lokaci zaka so ka yi mentioning na (wani) mutum, amma in baya cikin 'friendlist' naka, sai ya ƙi fitowa. Wani ma yana cikin ‘friendlist’ naka ɗin, amma ko ka so ‘mentioning’ nasa, sai ya ƙi fitowa.
Amma da zarar ka fara amfani da @ a farko, kafin sunansa, ko da kuwa page ne, sunan wannan mutumin, ko na page ɗin zai fito.
Misali:
@Muhammadu Buhari (Page)
@Audu Bulama Bukarti (Personal account)
@Bulama Adamu (Personal Account)
@Bulama Cartoons (Page)
Amfani da '@' (at sign) zai taimaka sosai wajen tallata kayan kasuwancinka a Social Media. Misali, idan kana tallata kaya, kuma kana da shafi, mentioning na page din kasuwancinka zai bawa mai karatu damar 'click/press' ya shiga shafin kai tsaye, misali:
@Elite Media NG
@Legend Textiles Ltd.
@Ace Konsult Ltd
@Lazeez Telecoms
2. # - HASHTAG
Amfanin amfani da #hashtag a social media shi ne, idan ka yi amfani da # a wata kalma (misali, #Hadejia), da zarar wanda ya ‘click/press’ a kan wannan #hashtag ɗin, zai sami sauran ‘postings’ da aka sa irin wannan kalmar mai #hashtag.
Misali:
• Suna:
#AnasDarazo
#AliyuMAhmad
#AliyuCares
• Maudu’i:
#KiwonLafiya
#FasaharZamani
#RayuwaDaNazari
#HikimominAnasDarazo
• Kayan Talla:
#EcoFertilizer
#Jallabiya
#Abaya
#Takalma
#Shadda
#maganingargajiya
#LogoDesign
• Jam’iyun Siyasa
#APC
#PDP
#NNPP
#LabourParty
✍️ Aliyu M. Ahmad
14th Dhul-Hijjah, 1443AH
13th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #FasaharZamani #SocialMedia #Hashtag #AtSign

0 Comments