Ka na ganin wani ya yi wata alfasha (a cikin hotuna, sauti ko hoto mai motsi), kuma ka ke yaÉ—awa da nufin nuna kuskurensa, to; kai ma ka taimaka wajen yaÉ—a alfashar.
Wataƙila! Da ba ka yaɗa ba, da, da yawa cikin masu bibiyarka ba za su ma san me mai wannan alfashar yake yi ba, balle su san shi, har wani ya fara bibiyarsa (following).
Wannan wata gaɓa ce da masu ƙoƙarin wayar da kai kan tarbiyya, addini da zamantakewa (musamman a social media) su kula da kyau, 'mentioning', ko 'screenshot'', ko 'video sharing' na wata ko wani maɓarnaci da za ka yaɗa da sunan gyara, yana ƙara ƙarfafa musu gwuiwa ne, kuma yana bawa followers naka damar bibiyarsu a karon farko. A Tiktok da Youtube zai ƙara musu watching time, hakan na nufin samun traffic, samun kuɗi, kai mai da'awa ka zama "referral" kenan, cikin rashin sani.
Ta wata fuskar nazarin halayya (psychology) kuma, duk abin da muke furtawa ko rubutu, É—ayan biyu ne, ko mun damu da abin, ko kuma abin ya dame mu.
Allah Ya ƙara mana shiriya!
Allah Ya mana tsari da taɓewa!
✍️ Aliyu M. Ahmad
30th Muharram, 1444AH
28th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDanazari #FasaharZamani
0 Comments