Mu azumci ranar Arfa, gobe Juma'a
1. Annabi ﷺ Ya kwaɗaitar da mummunai kan azumtar ranar Arfa, ga mazauna gida (waɗanda ba sa aikin Hajji), tare da albishir na, matuƙar aka yi azumin ya karɓu, akwai (yiwuwar) yafewa bawa zunubinsa na shekara 2 (sherar da ta wuce, da wacce zata zo) [Muslim, 2746].
2. Arfa ta bana (1443AH) ta zo a ranar Juma'a, akwai kuma hani da Manzon Allah ﷺ Ya yi kan azumtar ranar Juma'a ita kaɗai [Bukhari, 1849], SAI DAI 👇
Daga cikin bayanin da Malamai suka yi, ciki har da Ibn Hajr cikin Fathul Bari, abin da ake nufi da keɓe Juma'a da yin azumi shi ne; mutum ya ƙudurci yin azumin nafila, ba tare da sila ba a ranar Juma'a.
* Sila a misali, ranar Arfa, Shawwal, Azumin Annabi Dauda, Ramakon azumi, Tasi'u da Ashura, Ayyamul Bidh..
Saboda haka, ya halarta a azumci Arfa idan ranar ta faɗo a ranar Juma'a, WANNAN SANADI NE, ba wai keɓe Juma'ar aka yi da niyyar azumin nafila ba.
3. A ranar Arfa, ana a yawaita ADDU'A, ZIKIRI, KARATUN ALKUR'ANI MAI GIRMA, NEMAN GAFARAR ALLAH. Domin Arfa, yana daga cikin ranakun da Ubangiji ke gafartawa bayi [Muslim, 1348].
Allah Ya amsa mana ibadu, bukatun alheri 🤲
✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Dhul-Hijjah, 1443AH
7th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RanarArfa #DhulHijjah #Azumi
0 Comments