TARA APPS A WAYA

Tara ‘𝗮𝗽𝗽𝘀’ da yawa a (wasu) wayoyin yana da illa, amma ya danganta da wacce irin waya ce (𝗥𝗔𝗠, 𝗦𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲, 𝗕𝗮𝘁𝘁𝗲𝗿𝘆 da 𝘁𝘀𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗗𝗮𝘁𝗮). 

Wani lokacin muna tara '𝗮𝗽𝗽𝘀' barkatai a waya. Misali, a cikin '𝗮𝗽𝗽𝘀' 𝟭𝟬 in ka tattare su, sai ka ga guda 𝗯𝗶𝘆𝘂 ko ma ɗ𝗮𝘆𝗮𝗻 cikinsu kaɗai, zai iya wadatar da kai. Amma muna tara '𝗮𝗽𝗽𝘀' da yawa, suna 𝘇𝘂ƙ𝗲 𝗺𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝘁𝗮, suna 𝘀𝗵𝗮𝗻𝘆𝗲 𝗺𝗮𝗻𝗮 𝗰𝗮𝗷𝗶, suna sa wayoyinmu ɗ𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿 𝘇𝗮𝗳𝗶 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝘂𝘆𝗶. Duk da wani lokacin, muna amfani da wasu '𝗮𝗽𝗽𝘀' ɗin ne, saboda suna da wata '𝗳𝗲𝗮𝘁𝘂𝗿𝗲𝘀' da wasu ba su da ita.

𝟭. 𝗖𝗜𝗡𝗬𝗘 ‘𝗦𝗧𝗢𝗥𝗔𝗚𝗘’ (𝗦𝗣𝗔𝗖𝗘)

Kowanne '𝗮𝗽𝗽' na cikin wayarka yana da nauyinsa, gwargwadon yadda aka kirkire shi. Kowanne '𝗮𝗽𝗽' yana da kaso cikin '𝘀𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲' ɗin wayarka, wasu har da '𝗲𝘅𝗽𝗮𝗻𝘀𝗶𝗼𝗻 𝗳𝗶𝗹𝗲', wasu '𝗰𝗮𝗰𝗵𝗲𝘀', ga '𝗮𝗽𝗽 𝗱𝗮𝘁𝗮' yau da gobe.

Misali, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗵𝗿𝗼𝗺𝗲 a 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲 ko a 𝗔𝗽𝗽𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲, a 𝟮𝟱 𝗺𝗲𝗴𝗮 𝗯𝘆𝘁𝗲𝘀 (𝗮𝗽𝗽 𝘀𝗶𝘇𝗲) take. Amma da zaka sauƙe (installing) shi, ka yi kwana biyu kana amfani da shi, ka duba ‘𝗔𝗽𝗽 𝗜𝗻𝗳𝗼’, ciki wajen ‘𝗦𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲 𝗮𝗻𝗱 𝗖𝗮𝗰𝗵𝗲’, sai ka ga daga ta tafi kusan 𝟱𝟬𝟬𝗠𝗕 to 𝟭𝗚𝗕 saboda tara '𝗰𝗮𝗰𝗵𝗲𝘀'. Haka 𝗪𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽, 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸, 𝗪𝗣𝗦.... da sauransu.

𝟮. 𝗦𝗛𝗔𝗡𝗬𝗘 𝗖𝗔𝗝𝗜

Kowanne ‘𝗮𝗽𝗽’ da yake cikin wayarka yana amfani da 𝗰𝗮𝗷𝗶𝗻 𝗯𝗮𝘁𝘁𝗲𝗿𝘆 na wayar, sai dai wani ya fi wani sha (wani 17%, wani 5%, wani 0.09%...), ya danganta da yawan amfani da shi.

𝟯. 𝗦𝗛𝗔𝗡𝗬𝗘 𝗗𝗔𝗧𝗔

Kowanne ‘𝗮𝗽𝗽’ da yake cikin wayarka yana amfani da datar cikin wayarka, sai dai wani ya fi wani sha (wani a cikin 1GB, ya sha 200MB, wani 65MB, wani 10KB....) domin sabunta bayanai. 

𝟰. 𝗦𝗔𝗡𝗬𝗔 𝗪𝗔𝗬𝗔 𝗡𝗔𝗨𝗬𝗜 

Wannan kuma ya danga da 𝗥𝗔𝗠 na waya. Wata wayar in tana da kyakkyawan 𝗥𝗔𝗠, tara tarkacen ‘𝗮𝗽𝗽𝘀’ ba zai sanya ta yin nauyi ba, amma wata kam, zata rinka ƙamewa, saboda kaya sun yi mata yawa.

𝟱. 𝗦𝗔𝗡𝗬𝗔 𝗪𝗔𝗬𝗔 Ɗ𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥 𝗭𝗔𝗙𝗜

Bude '𝗮𝗽𝗽𝘀' da yawa a lokaci guda, yana daga cikin dalilan dake sa waya ɗaukar zafi (𝗪𝗮𝗻𝗶 𝗹𝗼𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗮𝘆𝗶 𝗻𝗲 (𝗻𝗮 𝘇𝗮𝗳𝗶/𝘇𝗮𝗳𝗶𝗻 𝗿𝗮𝗻𝗮), 𝗸𝗼 𝗺𝗮𝘁𝘀𝗮𝗹𝗮𝗿 𝗰𝗮𝗷𝗮). Dalili kuwa shi ne, kowanne '𝗮𝗽𝗽' a lokaci yana cikin amfani, yana 𝘀𝗵𝗮𝗻 𝗰𝗮𝗷𝗶, data da 𝗥𝗔𝗠, sai wayar ta dau ɗimi. Idan baka amfani da '𝗮𝗽𝗽', ta rufe shi, hatta daga minimizing (𝗿𝗲𝗰𝗲𝗻𝘁 𝘂𝘀𝗲/𝗮𝗰𝘁𝗶𝘃𝗶𝘁𝘆 𝗽𝗮𝗴𝗲).

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗞𝗜

Zaka yi tattalin data da caji, kuma wayarka zata laushi idan ka rage ‘𝗮𝗽𝗽𝘀’ da baka amfani da su, ko kuma kana da (wasu) madadinsu a wayarka, saboda waɗancan dalilan. 

• Ba sai ka haɗa 𝗖𝗵𝗿𝗼𝗺𝗲, 𝗙𝗶𝗿𝗲𝗳𝗼𝘅, 𝗢𝗽𝗲𝗿𝗮, 𝗘𝗱𝗴𝗲... a waya a ɗaya ba. Browser ɗaya (misali 𝗖𝗵𝗿𝗼𝗺𝗲) ta wadatar.

• Ba sai ka haɗa 𝗩𝗟𝗖, 𝗛𝗗 𝗩𝗶𝗱𝗲𝗼 𝗣𝗹𝗮𝘆𝗲𝗿, 𝗤𝗤 𝗣𝗹𝗮𝘆𝗲𝗿 a waya ɗaya ba. Player ɗaya (misali 𝗩𝗟𝗖) ta wadatar.

• Ba sai ka haɗa 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹, 𝗬𝗮𝗵𝗼𝗼 𝗠𝗮𝗶𝗹, 𝗢𝘂𝘁𝗹𝗼𝗼𝗸, 𝗘𝗺𝗮𝗶𝗹 𝗔𝗽𝗽... a waya ɗaya. Zaka iya ɗora kowanne irin 𝗺𝗮𝗶𝗹 a 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹, shi kaɗai ya wadatar.

• Ba sai ka haɗa 𝗕𝗲𝗮𝘂𝘁𝘆𝗣𝗹𝘂𝘀, 𝗣𝗵𝗼𝘁𝗼 𝗘𝗱𝗶𝘁𝗼𝗿 𝗣𝗿𝗼, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗦𝗻𝗮𝗽𝘀𝗲𝗲𝗱, 𝗣𝗵𝗼𝘁𝗼 𝗚𝗿𝗶𝗱, 𝗣𝗶𝘅𝗲𝗹, 𝗣𝗵𝗼𝘁𝗼 𝗦𝘁𝘂𝗱𝗶𝗼… iya 𝗦𝗡𝗔𝗣𝗦𝗘𝗘𝗗 za ta ma aikinsu gaba daya, koma fiye, ita shi kaɗai ta wadatar.

• 𝗪𝗣𝗦 𝗢𝗳𝗳𝗶𝗰𝗲 zai buɗe ma 𝗣𝗗𝗙𝘀 𝗳𝗶𝗹𝗲, 𝗪𝗼𝗿𝗱 𝗱𝗼𝗰𝘂𝗺𝗲𝗻𝘁, 𝗣𝗼𝘄𝗲𝗿 𝗣𝗼𝗶𝗻𝘁, 𝗦𝗽𝗿𝗲𝗲𝗱 𝗦𝗵𝗲𝗲𝘁 (𝗘𝘅𝗰𝗲𝗹), kai har “𝘀𝗰𝗮𝗻𝗻𝗶𝗻𝗴” yake na 𝗱𝗼𝗰𝘂𝗺𝗲𝗻𝘁 zuwa 𝗣𝗗𝗙… ba sai tara su A𝗔𝗱𝗼𝗯𝗲 𝗥𝗲𝗮𝗱𝗲𝗿 (𝗱𝗼𝗻 𝗯𝘂𝗱𝗲 𝗣𝗗𝗙𝘀), 𝗙𝗼𝘅𝗶𝘁 𝗥𝗲𝗮𝗱𝗲𝗿, 𝗖𝗮𝗺𝗦𝗰𝗮𝗻𝗻𝗲𝗿, 𝗣𝗗𝗙 converter…. 𝗪𝗣𝗦 kaɗai ya wadatar.

• Akwai wani ‘𝗮𝗽𝗽’ 𝗘𝗹-𝗠𝗼𝗵𝗮𝗳𝗲𝘇, shi kaɗai yana ɗauke da 𝗔𝗹𝗸𝘂𝗿’𝗮𝗻𝗶, 𝗦𝗮𝗵𝗶𝗵 𝗕𝘂𝗸𝗵𝗮𝗿𝗶, 𝗦𝗮𝗵𝗶𝗵 𝗠𝘂𝘀𝗹𝗶𝗺, 𝗔𝗿𝗯𝗮’𝘂𝗻𝗮 𝗔𝗻𝗻𝗮𝘄𝗮𝘄𝘆, 𝗨𝗺𝗱𝗮𝘁𝘂𝗹 𝗔𝗵𝗸𝗮𝗺, 𝗔𝗹-𝗝𝗮𝘇𝗮𝗿𝗲𝘆𝗮, 𝗔𝗹 𝗦𝗮𝗹𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹 𝗔𝗹 𝗦𝗵𝗮𝗳𝗶’, 𝗧𝘂𝗵𝗳𝗲𝘁 𝗔𝗹-𝗔𝘁𝗳𝗮𝗹, 𝗦𝗵𝗮𝘁𝗶𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮, 𝗔𝗹𝗯𝗮𝗾𝘂𝗻𝗶𝘆𝘆𝗮, 𝗔𝗹𝗾𝗮𝘄𝗮’𝗶𝗱𝘂𝗹 𝗙𝗶𝗾𝗵𝗶𝘆𝘆𝗮 da 𝗔𝗿𝗿𝗮𝗵𝗯𝗶𝘆𝘆𝗮. Kuma akwai na 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 (a 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲) da 𝗶𝗦𝗢/iPhone (a 𝗔𝗽𝗽𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲).*

• Akwai wani ‘𝗮𝗽𝗽’ na 𝗛𝗮𝗱𝗶𝘁𝗵 𝗖𝗼𝗹𝗹𝗲𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻𝘀 (na 𝗤𝘂𝗮𝗿𝘁𝗲𝗿 𝗣𝗶), na 𝗟𝗮𝗿𝗮𝗯𝗰𝗶 (𝗔𝗿𝗮𝗯𝗶𝗰) da 𝗧𝘂𝗿𝗮𝗻𝗰𝗶 (𝗘𝗻𝗴𝗹𝗶𝘀𝗵), yana ɗauke da 𝗕𝘂𝗸𝗵𝗮𝗿𝗶, 𝗠𝘂𝘀𝗹𝗶𝗺, 𝗔𝗯𝘂 𝗗𝗮𝘄𝘂𝗱, 𝗠𝘂𝘄𝗮𝘁𝘁𝗮 𝗠𝗮𝗹𝗶𝗸, 𝗡𝗮𝘀𝗮’𝗶, 𝗧𝗶𝗿𝗺𝗶𝗱𝗵𝗶, 𝗜𝗯𝗻 𝗠𝗮𝗷𝗮𝗵, 𝗥𝗶𝘆𝗮𝗱𝘂𝘀 𝗦𝗮𝗹𝗶𝗵𝗶𝗻, 𝗔𝗱𝗮𝗯𝘂𝗹 𝗠𝘂𝗳𝗿𝗮𝗱, 𝗦𝗵𝗮𝗺𝗮’𝗶𝗹, 𝗕𝘂𝗹𝘂𝗴𝗵𝘂𝗹 𝗠𝗮𝗿𝗮𝗺, 𝗔𝗿𝗯𝗮’𝘂𝗻𝗮 𝗛𝗮𝗱𝗶𝘀, duk cikin 𝗟𝗮𝗿𝗮𝗯𝗰𝗶 da 𝗧𝘂𝗿𝗮𝗻𝗰𝗶.*  

* Waɗannan '𝗮𝗽𝗽𝘀' ɗin kaɗai sun haɗa kusan ‘𝗮𝗽𝗽𝘀’ 12 - 15, sun kuma wadatar, ba sai ka sauƙe ɗaiɗaikunsu sun cika ma waya ba. 

✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱  
26th Dhul-Qaadah, 1443AH
26th June, 2022CE

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Hausa #MobileApp

Post a Comment

0 Comments