LURA DA FACEBOOK



Wani ba kwace ma 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 zai yi, a'a; zai na nemi damar shiga shafukanka ne domin yana bibiyar me kake, da kuma su wa kake mu'amala a 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸.

Zaka iya gane in ba kai kaɗai ke amfani da shafinka na 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 ba, ta waɗannan matakan:

1. Ka shiga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 𝗦𝗲𝘁𝘁𝗶𝗻𝗴.
2. Sai ka shiga '𝗦𝗲𝗰𝘂𝗿𝗶𝘁𝘆 𝗮𝗻𝗱 𝗟𝗼𝗴𝗶𝗻'
3. Ka shiga '𝗪𝗵𝗲𝗿𝗲 𝘆𝗼𝘂 𝗮𝗿𝗲 𝗹𝗼𝗴𝗴𝗲𝗱 𝗶𝗻'
4. Ka shiga '𝗦𝗲𝗲 𝗮𝗹𝗹', A nan zaka ga '𝗱𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲𝘀' (𝘄𝗮𝘆𝗮 ko 𝗰𝗼𝗺𝗽𝘂𝘁𝗲𝗿) da aka yi/ake amfani da su wajen shiga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 𝗔𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 naka.

* Misali, ni ina amfani da 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗣𝗶𝘅𝗲𝗹 𝟰𝗫𝗟 ko 𝗶𝗣𝗵𝗼𝗻𝗲 𝟭𝟭 𝗣𝗿𝗼 𝗠𝗮𝘅, ko 𝗪𝗶𝗻𝗱𝗼𝘄𝘀 𝗣𝗖 (𝗖𝗵𝗿𝗼𝗺𝗲/𝗙𝗶𝗿𝗲𝗳𝗼𝘅) wajen buɗe 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 ɗina, idan na ga wani '𝗱𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲' ba waɗannan ba, to tabbas wani yana bibiyar shafina.

5. Yadda zaka '𝗯𝗹𝗼𝗰𝗸𝗶𝗻𝗴' duk wani '𝗱𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲' da baka aminta da shi ba, shi ne; zaka '𝗽𝗿𝗲𝘀𝘀𝗶𝗻𝗴' akan wannan 3-dots "⋮" a kan kowanne 𝗱𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲 a cikin jerin "𝗪𝗵𝗲𝗿𝗲 𝘆𝗼𝘂 𝗮𝗿𝗲 𝗹𝗼𝗴𝗴𝗲𝗱 𝗶𝗻", zai ba ka zaɓi na '𝗹𝗼𝗴𝗼𝘂𝘁' a kan baƙon '𝗱𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲' dake amfani da 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 naka.


𝗞𝗔 𝗬𝗜 𝗦𝗔𝗡𝗜...

Matuƙar ba ka sa '𝘁𝘄𝗼 𝗳𝗮𝗰𝘁𝗼𝗿 𝗮𝘂𝘁𝗵𝗲𝗻𝘁𝗶𝗰𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻' a 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 ɗinka ba, za a iya shiga shafinka na 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 ba tare da saninka ba.

Duk wanda ya iya shiga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 acccount ɗinka, hakan zai ba shi damar:

1. Samu damar shiga ''𝗠𝗲𝘀𝘀𝗲𝗻𝗴𝗲𝗿', ya iya ganin '𝗰𝗵𝗮𝘁𝘀' naka.
2. Ganin 𝗵𝗶𝘀𝘁𝗼𝗿𝘆 na '𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴(s)' da kake a 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸, 𝘃𝗶𝗱𝗼𝗲𝘀 da ka kalla, ko 𝗽𝗼𝘀𝘁𝗶𝗻𝗴 da ka karanta. Zai iya ganin duk '𝗴𝗿𝗼𝘂𝗽(s)' da'𝗽𝗮𝗴𝗲𝘀' da kake bibiya (𝗳𝗼𝗹𝗹𝗼𝘄𝗶𝗻𝗴).
3. Zai samun damar ganin sauran bayanai da ka adana don kanka (𝗼𝗻𝗹𝘆 𝗺𝗲).
4. Zai iya yin '𝗰𝗵𝗮𝘁' ko '𝗽𝗼𝘀𝘁𝗶𝗻𝗴' a madadinka.

Ana iya samun masu bibiyar shafukanmu, cikin waɗanda muka aminta da su cikin abokai, masoya, ma'aurata da sauransu.

𝗬𝗔𝗗𝗗𝗔 𝗭𝗔𝗞𝗔 𝗦𝗔 𝗧𝗪𝗢 𝗙𝗔𝗖𝗧𝗢𝗥 𝗔𝗨𝗧𝗛𝗘𝗡𝗧𝗜𝗖𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡 𝗡𝗔 𝗙𝗔𝗖𝗘𝗕𝗢𝗢𝗞

1. Ka shiga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 𝗦𝗲𝘁𝘁𝗶𝗻𝗴
2. Sai ka shiga '𝗦𝗲𝗰𝘂𝗿𝗶𝘁𝘆 𝗮𝗻𝗱 𝗟𝗼𝗴𝗶𝗻'
2. Ka yi '𝙨𝙘𝙧𝙤𝙡𝙡𝙞𝙣𝙜' ƙasa, akwai '𝗧𝘄𝗼-𝗳𝗮𝗰𝘁𝗼𝗿 𝗔𝘂𝘁𝗵𝗲𝗻𝘁𝗶𝗰𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻'
4. Ka zaɓi na 'biyu' 𝗧𝗘𝗫𝗧 𝗠𝗘𝗦𝗦𝗔𝗚𝗘 (𝗦𝗠𝗦)', sai ka yi '𝗖𝗼𝗻𝘁𝗶𝗻𝘂𝗲'
5. Ka sa 𝗹𝗮𝗺𝗯𝗮𝗿 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿𝗸𝗮, za su turo ma da '𝗰𝗼𝗻𝗳𝗶𝗿𝗺𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻 𝗰𝗼𝗱𝗲' mai lambobi guda shida (6).
6. Bayan ka sa wancan '𝗰𝗼𝗻𝗳𝗶𝗿𝗺𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻 𝗰𝗼𝗱𝗲', sai ka yi '𝗖𝗼𝗻𝘁𝗶𝗻𝘂𝗲', ka sa '𝗽𝗮𝘀𝘀𝘄𝗼𝗿𝗱' na 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸.
7. Sai ka yi '𝗗𝗼𝗻𝗲', shikenan.

𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗜 𝗧𝗪𝗢-𝗙𝗔𝗖𝗧𝗢𝗥 𝗔𝗨𝗧𝗛𝗘𝗡𝗧𝗜𝗖𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡 𝗔 𝗙𝗔𝗖𝗘𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗦𝗛𝗜 𝗡𝗘

1. Yana da matuƙar wuya a iya hacking na shafinka a 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸.
2. Ko mutum ya san '𝗽𝗮𝘀𝘀𝘄𝗼𝗿𝗱' na ka, ba zai iya shiga shafin 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸 naka ba, saboda sai sun tura ma '𝗰𝗼𝗻𝗳𝗶𝗿𝗺𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻 𝗰𝗼𝗱𝗲.'

NB:
𝘼𝙣𝙖 𝙞𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙢𝙖𝙨𝙪 𝙗𝙞𝙗𝙞𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙝𝙖𝙛𝙪𝙠𝙖𝙣𝙢𝙪, 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣 𝙬𝙖ɗ𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙖 𝙖𝙢𝙞𝙣𝙩𝙖 𝙙𝙖 𝙨𝙪, 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣 𝙖𝙗𝙤𝙠𝙖𝙞, 𝙢𝙖𝙨𝙤𝙮𝙖, 𝙢𝙖'𝙖𝙪𝙧𝙖𝙩𝙖 𝙙𝙖 𝙨𝙖𝙪𝙧𝙖𝙣𝙨𝙪. 𝙈𝙪 𝙠𝙞𝙮𝙖𝙮𝙚 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙧 𝙙𝙖 𝙂𝙢𝙖𝙞𝙡 𝙙𝙖 𝙥𝙖𝙨𝙨𝙬𝙤𝙧𝙙 ɗ𝙞𝙣𝙨𝙖, 𝙠𝙤 𝙬𝙖𝙮𝙤𝙮𝙞𝙣𝙢𝙪 𝙖 𝙝𝙖𝙣𝙣𝙪𝙣𝙢𝙪 𝙢𝙪𝙩𝙖𝙣𝙚 𝙗𝙖𝙧𝙠𝙖𝙩𝙖𝙞.

✍️ Aliyu M. Ahmad
1st Dhul-Hijjah, 1443AH
30th June, 2022CE

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Facebook #Hacking #PrivacyProtection #Hausa #MobileApp

 



  

 

 





 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments