XENDER


𝗫𝗘𝗡𝗗𝗘𝗥 manhajar ce da muka fi sani wajen yin ‘𝘁𝗿𝗮𝗻𝘀𝗳𝗲𝗿’ na ‘𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀’ (𝙞𝙙𝙚𝙤𝙨, 𝙖𝙪𝙙𝙞𝙤𝙨, 𝙥𝙝𝙤𝙩𝙤𝙨, 𝙖𝙥𝙥𝙨, 𝙙𝙤𝙘𝙪𝙢𝙚𝙣𝙩𝙨...) daga wata wayar zuwa wata waya, a tsakanin 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 da 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱, ko 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 da 𝗶𝗣𝗵𝗼𝗻𝗲, ko tsakanin 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 da 𝗞𝗮𝗶𝗢𝗦, ko tsakanin 𝘄𝗮𝘆𝗮 da 𝗰𝗼𝗺𝗽𝘂𝘁𝗲𝗿. 

Akwai kuma wasu muhimman aiyuka da za mu iya da 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿 wanɗanda suka haɗa da:

1. Sauƙe 𝘀𝘁𝗮𝘁𝘂𝘀 na 𝗪𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽
2. Sauƙe '𝘃𝗶𝗱𝗲𝗼' daga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸, 𝗧𝘄𝗶𝘁𝘁𝗲𝗿 da 𝗜𝗻𝘀𝘁𝗮𝗴𝗿𝗮𝗺
3. 𝗖𝗼𝗻𝘃𝗲𝗿𝘁𝗶𝗻𝗴 na ‘𝗩𝗶𝗱𝗲𝗼’ zuwa‘𝗔𝘂𝗱𝗶𝗼’
4. Maida kayan (files) na tsohuwar waya zuwa sabuwar waya (𝗰𝗹𝗼𝗻𝗶𝗻𝗴)

𝟭. 𝗦𝗔𝗨Ƙ𝗘 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗨𝗦 𝗡𝗔 (𝗩𝗜𝗗𝗘𝗢 𝗞𝗢 𝗣𝗛𝗢𝗧𝗢) 𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗪𝗛𝗔𝗧𝗦𝗔𝗣𝗣

Kafin ka sauƙe ‘𝘀𝘁𝗮𝘁𝘂𝘀’ na 𝗪𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽 ta hanyar amfani da 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿, sai  ka buɗe (𝘀𝘁𝗮𝘁𝘂𝘀 𝘃𝗶𝗲𝘄𝗶𝗻𝗴) ta 𝗪𝗵𝗮𝘁𝘀𝗮𝗽𝗽 da farko tukun.

Sai ka shiga cikin 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿, ka duba can ƙasa, zaka ga ‘social’, sai ka shiga ‘𝗦𝗼𝗰𝗶𝗮𝗹’. Duk '𝘀𝘁𝗮𝘁𝘂𝘀es' da ka buɗe za su fito a nan, sai ka zaɓa, ka yi '𝘀𝗮𝘃𝗶𝗻𝗴.' 

𝟮. 𝗦𝗔𝗨Ƙ𝗘 𝗩𝗜𝗗𝗘𝗢 𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗙𝗔𝗖𝗘𝗕𝗢𝗢𝗞, 𝗧𝗪𝗜𝗧𝗧𝗘𝗥 𝗗𝗔 𝗜𝗡𝗦𝗧𝗔𝗚𝗥𝗔𝗠

Idan kana buƙatar 𝘀𝗮𝘂ƙ𝗲 (downloading) na wani '𝘃𝗶𝗱𝗲𝗼' daga 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸, 𝗧𝘄𝗶𝘁𝘁𝗲𝗿 ko 𝗜𝗻𝘀𝘁𝗮𝗴𝗿𝗮𝗺 ta hanyar amfani da 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿 ga matakan da zaka bi:

• Zaka yi '𝗰𝗼𝗽𝘆𝗶𝗻𝗴' na 𝗹𝗶𝗻𝗸 ɗin wannan videon.
• Sai ka buɗe 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿, ka shiga wannan wajen na ‘𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗟’
• Sai ka shiga wajen da aka rubuta ‘𝗣𝗮𝘀𝘁𝗲 𝗮𝗻𝗱 𝗗𝗼𝘄𝗻𝗹𝗼𝗮𝗱’, sai ka buɗe, ka yi ‘𝗽𝗮𝘀𝘁𝗶𝗻𝗴’ na wancan 𝗹𝗶𝗻𝗸 da ka yi 𝗰𝗼𝗽𝘆𝗶𝗻𝗴 ɗin.
• Zai yi '𝗮𝗻𝗮𝗹𝘆𝘇𝗶𝗻𝗴' na 𝗹𝗶𝗻𝗸 ɗin na lokaci kaɗan, sai kuma ya fara 𝗱𝗼𝘄𝗻𝗹𝗼𝗮𝗱𝗶𝗻𝗴.

𝟯. 𝗖𝗢𝗡𝗩𝗘𝗥𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗡𝗔 ‘𝗩𝗜𝗗𝗘𝗢’ 𝗭𝗨𝗪𝗔 ‘𝗔𝗨𝗗𝗜𝗢’

Ana iya amfani da 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿 wajen ‘coverting’ na ‘video’ ya koma ‘audio’ ta waɗannan matakan:

• Ka shiga cikin ‘𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿’
• Ka duba daga ƙasa, zaka ga waje wani ‘𝗯𝗼𝘁𝘁𝗼𝗺’ an rubuta '𝗧𝗼𝗠𝗽𝟯', sai ka shiga ciki.
• A ciki, zai baka zaɓi guda 2. Na farko, 𝗧𝗼𝗠𝗽𝟯, na na biyu kuma 𝗟𝗢𝗖𝗔𝗟. Zaka iya shiga ta kowannensu, don nemo/zaɓar 𝘃𝗶𝗱𝗲𝗼𝗻 da kake son maidawa 𝗠𝗣𝟯 (𝗮𝘂𝗱𝗶𝗼/𝘀𝗮𝘂𝘁𝗶). 

𝟰. 𝗠𝗔𝗜𝗗𝗔 𝗙𝗜𝗟𝗘𝗦 𝗡𝗔 𝗧𝗦𝗢𝗛𝗨𝗪𝗔𝗥 𝗪𝗔𝗬𝗔 𝗭𝗨𝗪𝗔 𝗦𝗔𝗕𝗨𝗪𝗔𝗥 𝗪𝗔𝗬𝗔 

𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿 tana da tsarin 𝗖𝗟𝗢𝗡𝗘, tsari ne da zai baka damar ‘𝘁𝗿𝗮𝗻𝘀𝗳𝗲𝗿’ na 𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀, 𝗮𝗽𝗽𝗹𝗶𝗰𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻𝘀, 𝗰𝗼𝗻𝘁𝗮𝗰𝘁𝘀... daga wata wayar zuwa wata wayar.

Wannan tsarin na 𝗖𝗟𝗢𝗡𝗘 zai baka damar ɗebe kayan tsohuwar wayarka, zuwa sabuwa ba tare da ka rasa komai ba, ciki har da '𝗺𝗲𝘀𝘀𝗮𝗴𝗲𝘀' da '𝗰𝗮𝗹𝗹 𝗵𝗶𝘀𝘁𝗼𝗿𝘆'.

Yadda zaka yi amfani da wannan tsarin na 𝗫𝗘𝗡𝗗𝗘𝗥 𝗖𝗟𝗢𝗡𝗘 shi ne:

• Ka duba cikin 𝗫𝗲𝗻𝗱𝗲𝗿 da kyau, daga can sama (ɓangaren dama) akwai wani 𝗶𝗰𝗼𝗻 ≡, sai ka shige shi.
• A menu ɗin, ka duba na ƙarshe, shi ne "𝗣𝗵𝗼𝗻𝗲 𝗖𝗼𝗽𝘆", sai ka shige shi.
• Sai ka zaɓa a cikin wayoyin biyu, ɗaya 𝗡𝗘𝗪 (wacce za a turawa), daya kuma 𝗢𝗟𝗗 (wacce za a transfer na files daga ita zuwa NEW).

Allah Ya amfana!

✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱 
23rd Dhul-Qaadah, 1443AH
23rd June, 2022CE 

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Xender #Hausa

Post a Comment

0 Comments