𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼(𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲) ɗaya ne daga cikin manhajojin Google. 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼 kai tsaye za mu iya cewa "File Manager' ne,
Wasu daga cikin wayoyin Android na 𝗣𝗶𝘅𝗲𝗹, 𝗧𝗲𝗰𝗻𝗼, 𝗜𝗻𝗳𝗶𝗻𝗶𝘅, 𝗜𝘁𝗲𝗹... suna zuwa da shi. In kuma kana buƙata, zaka iya ɗauko shi a 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲 (bit.ly/3HQuv65).
Shi wannan application, aikinsa ba iya ajiye '𝗳𝗶𝗹𝗲' ba ne, ko '𝗰𝗼𝗽𝘆' and '𝗽𝗮𝘀𝘁𝗲', ko '𝗱𝗲𝗹𝗲𝘁𝗶𝗻𝗴' na file. 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼 yana da wasu ɓoyayyun aiyuka.
1. Idan ka gode file a 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼, baya tafiya kai-tsaye, idan ka yi '𝗺𝗼𝘃𝗲 𝘁𝗼 𝗯𝗶𝗻'. Zai ajiye ma file ɗin a '𝗥𝗘𝗖𝗬𝗖𝗟𝗜𝗡𝗚 𝗕𝗜𝗡' (kamar irin na computer).
Zai ajiye ma files da ka yi delete na tsawon kwanaki 60, bayan kwana 60 in baka dawo da file(s) ɗin ba, zai goge da kansa.
2. Ta 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼 ana iya transfer na 'files' kamar a Xender.
3. Yana da '𝗦𝗮𝗳𝗲 𝗙𝗼𝗹𝗱𝗲𝗿', ma'ana, inda ka iya ajiye wani files, tare da sanyawa 'folder' din '𝘀𝗲𝗰𝘂𝗿𝗶𝘁𝘆 𝗰𝗼𝗱𝗲'.
4. Da 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼, ana iya goge '𝗷𝘂𝗻𝗸𝘀' (duk wasu abubuwa marasa amfani) don karin samun spaces a cikin waya.
5. Ta kan wannan mahajar ta 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼, zaka iya playing na '𝘃𝗶𝗱𝗲𝗼𝘀' da '𝗮𝘂𝗱𝗶𝗼' ba tare da ka tara tarkacen '𝗽𝗹𝗮𝘆𝗲𝗿𝘀' a wayarka ba.
6. Da 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀 𝗚𝗼, kai tsaye zaka iya maida '𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀' dinka kan '𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗗𝗿𝗶𝘃𝗲'.
𝗔𝗕𝗜𝗡 𝗟𝗨𝗥𝗔:
Akwai (wasu) tarin '𝗮𝗽𝗽𝘀' a cikin wayoyinmu da suke iya wadatar sa mu aiyukan wasu '𝗮𝗽𝗽𝘀' din, ba sai mun tara tarkacen wasu '𝗮𝗽𝗽𝘀' din ba, sun cinye mana '𝘀𝗽𝗮𝗰𝗲/𝘀𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲', shanye mana '𝗯𝗮𝘁𝘁𝗲𝗿𝘆' da kuma cin '𝗯𝗮𝗰𝗸𝗴𝗿𝗼𝘂𝗻𝗱 𝗱𝗮𝘁𝗮'.
✍️ Aliyu M. Ahmad
26th Dhul-Qaadah, 1443AH
26th June, 2022CE
#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Google #GoogleApp #Hausa #MobileApp
0 Comments