𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗜𝗡 𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗔𝗥 𝗚𝗠𝗔𝗜𝗟 (𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗔𝗖𝗖𝗢𝗨𝗡𝗧)


Kamar yadda bayani ya gabata, 𝗚𝗠𝗔𝗜𝗟 ɗaya ne daga cikin “𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹 𝘀𝗲𝗿𝘃𝗶𝗰𝗲 𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿” da kamfanin 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 ke gudanar da shi. Ga mai amfani da 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱, ‘𝗲𝗺𝗮𝗶𝗹’ na 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 (𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹) zai fi yi masa amfani fiye da saura ‘𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿𝘀’ na 𝗬𝗮𝗵𝗼𝗼, 𝗛𝗼𝘁𝗺𝗮𝗶𝗹, 𝗬𝗮𝗻𝗱𝗲𝘅 da sauransu.

  

Da yawan mutane in an ce 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲, sukan taƙaita shi da ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴 𝗲𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲’ ma'ana 𝙬𝙪𝙧𝙞𝙣 𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙠𝙖 𝙗𝙧𝙤𝙬𝙨𝙞𝙣𝙜 (𝙗𝙞𝙣𝙘𝙞𝙠𝙚) 𝙣𝙖 𝙖𝙣𝙞 𝙖𝙗𝙪; in kuma aka ambaci ‘𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹’, da yawa mukan taƙaita aikinsa da turawa ko karɓar ‘email’; amma duk 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶𝗻𝘀𝘂 𝘆�� 𝘄𝘂𝗰𝗲 𝗻𝗮𝗻.

 

𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 shi ne kamfanin da yafi kowanne kamfani ƙarfi a duniyar fasahar sadarwa. Shi ne kamfani da yake gudanar da 𝗢𝗦 (𝗼𝗽𝗲𝗿𝗮𝘁𝗶𝗻𝗴 𝘀𝘆𝘀𝘁𝗲𝗺) na 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 tare da shi da sauran wasu kamfanoni. 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 shi ne 𝗢𝗦 da mafi yawancinmu muka fi amfani da shi a wayoyinmu na 𝗦𝗮𝗺𝘀𝘂𝗻𝗴, 𝗣𝗶𝘅𝗲𝗹, 𝗧𝗲𝗰𝗻𝗼, 𝗜𝗻𝗳𝗶𝗻𝗶𝘅, 𝗜𝘁𝗲𝗹, 𝗫𝗶𝗮𝗼𝗺𝗶, 𝗚𝗶𝗼𝗻𝗲𝗲, 𝗛𝘂𝗮𝘄𝗲𝗶, 𝗛𝗧𝗖, 𝗠𝗼𝘁𝗼𝗿𝗼𝗹𝗹𝗮, 𝗢𝗽𝗽𝗼, 𝗡𝗼𝗸𝗶𝗮, 𝗩𝗶𝘃𝗼 da sauransu.

 

1. Idan ka buɗe ‘𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁' kai tsaye ka yi rijista ne ‘𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗔𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 𝗮𝗻𝗱 𝗦𝗲𝗿𝘃𝗶𝗰𝗲𝘀', ma’ana zaka ya amfani da duk wani tsare-tsare da 𝗺𝗮𝗻𝗵𝗮𝗷𝗼𝗷𝗶𝗻 𝟭𝟯𝟭 da 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 ke gudanar da su (about.google/products), waɗanda iya mai 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 ne kaɗai zai iya morarsu kai tsaye 100%. 

 

Waɗanan manhajojin sun haɗa da 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹, 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲, 𝗬𝗼𝘂𝘁𝘂𝗯𝗲, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗗𝗿𝗶𝘃𝗲, 𝗣𝗵𝗼𝘁𝗼𝘀, 𝗕𝗹𝗼𝗴𝗴𝗲𝗿, 𝗙𝗼𝗿𝗺𝘀, 𝗔𝗹𝗲𝗿𝘁𝘀, 𝗔𝗱𝗦𝗲𝗻𝘀𝗲, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗵𝗮𝘁𝘀, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗹𝗮𝘀𝘀𝗿𝗼𝗼𝗺, 𝗙𝗮𝗺𝗶𝗹𝘆 𝗟𝗶𝗻𝗸, 𝗙𝗶𝗻𝗱 𝗠𝘆 𝗗𝗲𝘃𝗶𝗰𝗲, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗚𝗿𝗼𝘂𝗽𝘀, 𝗖𝗼𝗻𝘁𝗮𝗰𝘁𝘀, 𝗠𝗲𝘀𝘀𝗮𝗴𝗲, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗢𝗻𝗲, 𝗣𝗼𝗱𝗰𝗮𝘀𝘁, 𝗛𝗮𝗻𝗴𝗼𝘂𝘁𝘀, 𝗦𝗰𝗵𝗼𝗹𝗮𝗿, 𝗠𝗲𝗲𝘁, 𝗔��𝗠𝗼𝗯, 𝗖𝗹𝗼𝘂𝗱, 𝗧𝗿𝗮𝗻𝘀𝗹𝗮𝘁𝗲… da sauransu. Kuma ana amfani da su waje sadar da sakwanni, karatu, kasuwanci, developing, taruka, adana bayanai, ƙididdiga da sauransu.

 

2. Mallakar '𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁' yana taimakawa wajen 𝗔𝗨𝗧𝗢-𝗙𝗜��𝗟 na l𝗹𝗼𝗴𝗶𝗻 𝗰𝗿𝗲𝗱𝗲𝗻𝘁𝗶𝗮𝗹𝘀 (bayanai da zaka shiga domin buɗe wani shafi, i.e. 𝘂𝘀𝗲𝗿𝗻𝗮𝗺𝗲 da 𝗽𝗮𝘀𝘀𝘄𝗼𝗿𝗱𝘀); ma’ana, idan ka yi 𝘀𝗮𝘃𝗶𝗻𝗴 bayanan shiga wani shafi (mis. 𝗙𝗮𝗰𝗲𝗯𝗼𝗼𝗸, ko 𝗧𝘄𝗶𝘁𝘁𝗲𝗿), babu buƙatar sai ka yi 𝘁𝘆𝗽𝗶𝗻𝗴 na 𝘂𝘀𝗲𝗿𝗻𝗮𝗺𝗲 da 𝗽𝗮𝘀𝘀𝘄𝗼𝗿𝗱, a’a kai tsaye 𝗔𝗨𝗧𝗢𝗙𝗜𝗟𝗟 zai shigar ma da bayanan.  

 

Ba za mu iya bayanin dukkan ‘𝗮𝗽𝗽𝘀’ 131 a yanzu ba, ba kuma lalle a ce sai ka iya amfani da dukkanin '𝗮𝗽𝗽𝘀' ɗin ba (𝘆𝗮 𝗱𝗮𝗻𝗴𝗮��𝗮 𝗱𝗮 𝗯𝘂ƙ𝗮𝘁𝗮 𝗻𝗲), sannan wasun su ba a iya amfani da su a wasu ƙasashen. 𝗚𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗶𝗻 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗮 𝘁𝗮ƙ𝗮𝗶𝗰𝗲:

 

𝗣𝗟𝗔𝗬𝗦𝗧𝗢𝗥𝗘 – rumbu ne mai ɗauke da manhajojin A𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 (𝗮𝗽𝗸) 𝟮.𝟱𝟵 𝗺𝗶𝗹𝗹𝗶𝗼𝗻 (Statista, 2022). Mai 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 (𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹) ne kaɗai ne zai iya shiga domin sauƙe '𝗮𝗽𝗽𝘀' daga cikin 𝗣𝗹𝗮𝘆𝘀𝘁𝗼𝗿𝗲

 

𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗖𝗢𝗡𝗧𝗔𝗖𝗧𝗦 - ‘𝗮𝗽𝗽’ ne da ake iya adana 𝗹𝗮𝗺𝗯𝗼𝗯𝗶𝗻 𝘄𝗮𝘆𝗮 daga 𝟭 zuwa 𝟮𝟱,𝟬𝟬𝟬. Amfani da '𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗼𝗻𝘁𝗮𝗰𝘁' na da matuƙar muhimmanci, saboda ko an sami akasi wayarka 𝘁𝗮 ɓ𝗮𝘁𝗮, ko 𝘁𝗮 𝗹𝗮𝗹𝗮𝗰𝗲, ko 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗰𝗲, da zarar ka sami wata 𝘄𝗮𝘁𝗮 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿 ko 𝗮 𝗰𝗼𝗺𝗽𝘂𝘁𝗲𝗿 zaka iya dawo da duk ‘𝗰𝗼𝗻𝘁𝗮𝗰𝘁𝘀’ da ka adana (𝘀𝗮𝘃𝗶𝗻𝗴) cikinsa.

 

𝗕𝗟𝗢𝗚𝗚𝗘𝗥 – zaka iya ƙirƙirar '𝗯𝗹𝗼𝗴 𝘀𝗶𝘁𝗲' da 𝗕𝗹𝗼𝗴𝗴𝗲𝗿, har kana iya wallafa rubutu kyauta. Idan kana samun 𝘁𝗿𝗮𝗳𝗳𝗶𝗰 da yawa, zaka iya ‘𝗿𝗶𝗷𝗶𝘀𝘁𝗮’ da ‘𝗔𝗱𝘀𝗲𝗻𝘀𝗲’ ka fara samun kudin da Blogger idan kana ɗora talla/ads (misali, aliyumahmad.blogspot.com).

 

𝗙𝗜𝗡𝗗 𝗠𝗬 𝗗𝗘𝗩𝗜𝗖𝗘 - manhaja ce da za ta taimaka wajen gano inda wayarka take, in 𝗸𝗮 𝗿𝗮𝘀𝗮 𝘁𝗮, ko 𝗸𝗮 𝗷𝗲𝗳𝗮𝗿, ko 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗰𝗲

 

𝗬𝗢𝗨𝗧𝗨𝗕𝗘 – wannan sananne ‘𝗮𝗽𝗽’ ne na Google da zaka iya buɗe ‘𝗰𝗵𝗮𝗻𝗻𝗲𝗹’ a shi ta hanyar amfani da ‘𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗔𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁'. Idan kana samun 𝘁𝗿𝗮𝗳𝗳𝗶𝗰 da yawa, aƙalla 𝘀𝘂𝗯s𝗰𝗿𝗶𝗯𝗲𝗿𝘀 𝟭𝟬𝟬𝟬, kuma aka samu an buɗe ‘𝗰𝗼𝗻𝘁𝗲𝗻𝘁𝘀’ naka kamar sau 𝟰𝟬𝟬𝟬, zaka iya fara samun kuɗi da 𝗬𝗼𝘂𝘁𝘂𝗯𝗲

 

𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗣𝗛𝗢𝗧𝗢𝗦 – Wannan manhajar tana taimakawa sosai wajen adana hotunan cikin waya. Idan kana ‘𝗯𝗮𝗰𝗸𝘂𝗽’ na hotuna a cikin ‘𝗣𝗛𝗢𝗧𝗢𝗦’ za a iya ‘𝗿𝗲𝘀𝘁𝗼𝗿𝗶𝗻𝗴’ nasu a kowacce irin waya ka canja, a kowanne lokaci.

 

𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗗𝗥𝗜𝗩𝗘 – wannan manhajar ‘𝗰𝗹𝗼𝘂𝗱’ ce da ke iya bawa mutum damar ajiye ‘𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀’ a ciki. Suna bawa kowanne user (mutum) ‘𝘀𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲’ na 𝟭𝟱 𝗴𝗶𝗴𝗮𝗯𝘆𝘁𝗲𝘀. Zaka iya buɗe abubuwa da ka adana a cikin Drive a kowacce waya ko computer idan ka yi amfani da '𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗔𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁' (𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹) naka.

 

𝗦𝗖𝗛𝗢𝗟𝗔𝗥 - Google scholar kamar ‘𝗚��𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗦𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴 𝗘𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲’ ne. Yana taimaka wajen lalubo 𝗺𝗲𝘁𝗮𝗱𝗮𝘁𝗮 (ta rubuce-rubuce na ilimi). 

 

Misali, in ka sami wani rubutu, kuma kana son ba shi '𝗿𝗲𝗳𝗲𝗿𝗲𝗻𝗰𝗲' idan ka ɗauki '𝗷𝘂𝗺𝗹𝗮' ka ɗora a 𝗦𝗰𝗵𝗼𝗹𝗮𝗿 zai baka idan irin wannan jumlar ta bayyana a rubuce-rubuce da suka gabata, cikin 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗮𝗶, ko 𝗺𝘂ƙ𝗮𝗹𝗮 (𝗮𝗿𝘁𝗶𝗰𝗹𝗲𝘀), ko 𝗷𝗼𝘂𝗿𝗻𝗮𝗹𝘀, ko 𝗺𝘂𝗷𝗮𝗹𝗹𝗮 da sauransu.

 

𝗖𝗛𝗥𝗢𝗠𝗘 𝗥𝗘𝗠𝗢𝗧𝗘 𝗗𝗘𝗦𝗞𝗧𝗢𝗣 – manhaja ce da zata baka damar shiga cikin 𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀 na 𝗰𝗼𝗺𝗽𝘂𝘁𝗲𝗿 daga wayarka, koda baka tare da computer ɗin.

 

𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗔𝗗𝗦 – Manhajar 𝗔𝗱𝗦𝗲𝗻𝘀𝗲 da 𝗔𝗱𝗠𝗼𝗯 na taimakawa masu amfani a social media yin rijista domin 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗸𝘂ɗ𝗶 ta hanyar ɗora 𝘁𝗮𝗹𝗹𝗮 a shafukansu (ads).

 

𝗠𝗘𝗘𝗧𝗦 – kamar 𝗭𝗼𝗼𝗺 yake, ana yi 𝗺𝗲𝗲𝘁𝗶𝗻𝗴 𝗼𝗻𝗹𝗶𝗻𝗲

 

Akwai sauran 𝗮𝗽𝗽𝘀 na 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 da za su taimaka sosai wajen 𝗱𝗲𝘃𝗲𝗹𝗼𝗽𝗶𝗻𝗴, kamar 𝗢𝗽𝘁𝗶𝗺𝗶𝘇𝗲𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗔𝗻𝗮𝗹𝘆𝘁𝗶𝗰𝘀, 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗹𝗼𝘂𝗱, 𝗙𝗶𝗿𝗲𝗯𝗮𝘀𝗲, 𝗙𝗹𝘂𝘁𝘁𝗲𝗿, 𝗣𝗹𝗮𝘆 𝗣𝗿𝗼𝘁𝗲𝗰𝘁, 𝗣𝗹𝗮𝘆 𝗚𝗮𝗺𝗲𝘀, 𝗦𝘂𝗿𝘃𝗲𝘆, 𝗪𝗲𝗯 da sauransu. 

 

Akwai 𝗮𝗽𝗽𝘀 na 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 da za su taimaka wajen editing na hoto, 𝗦𝗡𝗔𝗣𝗦𝗘𝗘𝗗 da 𝗣𝗛𝗢𝗧𝗢𝗦. Akwai na duba 𝘁𝗮𝘀��𝗶𝗿𝗮 (𝗺𝗮𝗽), 𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗠𝗔𝗣 da 𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗘𝗔𝗥𝗧𝗛. Akwai manhajar karɓar bayanai ta 𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘 𝗙𝗢𝗥𝗠𝗦,, akwai manhajar fassara ta 𝗧𝗥𝗔𝗡𝗦𝗟𝗔𝗧𝗘. Akwai manhajoji da yawa na 𝗚𝗢𝗢𝗚𝗟𝗘, sai a hankali ko in buƙata ta tashi, za mu dauki wasu muna bayaninsu a taƙaice.

 

𝗔𝗕𝗜𝗡 𝗟𝗨𝗥𝗔:

 

1. Yawancin waɗancan tsare-tsare na 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲, iya masu 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗮𝗰𝗰𝗼𝘂𝗻𝘁 (𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹) ke iya morarsu 100%. 

 

2. Ana iya amfani da 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹, kamar sauran ‘𝗽𝗿𝗼𝘃𝗶𝗱𝗲𝗿𝘀’ (𝗬𝗮��𝗼𝗼, 𝗛𝗼𝘁𝗺𝗮𝗶𝗹…) wajen yin 𝗿𝗶𝗷𝗶𝘀𝘁𝗮 ko 𝗰𝗶𝗸𝗲-𝗰𝗶𝗸𝗲𝗻 da ake a 𝘆𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗴𝗶𝘇𝗼, kamar buɗe 𝗽𝗿𝗼𝗳𝗶𝗹𝗲 na makaranta ko cike aiki (𝗷𝗼𝗯 𝗮𝗽𝗽𝗹𝗶𝗰𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻, kamar na sojoji da sauransu), ko cike 𝘁𝗮𝗹𝗹𝗮𝗳𝗶 (mis. 𝗦𝘂𝗿𝘃𝗶��𝗮𝗹 𝗙𝘂𝗻𝗱) da sauran cike-cike. 

 

3. Kar ka yi gangacin bawa kowa 𝗹𝗼𝗴𝗶𝗻 𝗱𝗲𝘁𝗮𝗶𝗹𝘀 na 𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹 naka, domin za a iya shiga (𝗮𝗰𝗰𝗲𝘀𝘀𝗶𝗻𝗴) dukkan waɗancan tsare-tsaren da shi. 

 

Description: ✍️Aliyu M. Ahmad

22nd Dhul-Qaadah, 1443AH

20ndJune, 2022CE 

 

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Gmail #Mail #Hausa

 

Post a Comment

0 Comments