A tsakiyar Miladiyyar 1920, wakilin birnin Alwar na Indiyya, Jai Singh Prabhaka ya ziyarci birnin London. A cikin wata safiya ya fito domin ya zaga cikin birni, isowarsa titin Mayfair, ya iske wani wajen sayar da motoci. Sarki ya Æ™arasa wajen, ya shiga ofishin babban dillalin motoci, ya tambaye shi kan; ya bashi farashi da bayanan motar Rolls-Royce (motar da kudinta ya kai ₦260 millions a kuÉ—in Nijeriya).
Nan Dillalin motar ya yi masa tsawa, da ba'a, tare da cewa "ya tafi ya bashi wuri, kar ya ɓata masa lokaci, bai ga alamun iya siyan mota a tattare da shi ba." Cikin rashin sanin cewa Sir. Jai Singh, ba gama-garin mutum ba ne, Sir Jai Singh ya juya ya tafi.
Bayan Sir. Jai Singh ya koma masauƙinsa (a hotel), sai ya turo yaronsa wannan wajen sayar da motocin, ya ce a faɗa musu, wani babban Sarki daga Indiya yana so zai zo ya sayi motoci a wajensu. Nan da nan, aka sa ma'aikata suka gyara wajen, kana aka kawo jan karfet aka shimfiɗa.
Shigar Sarki Jai Singh cikin 'garejin ajiye motocin', ya tarar Rolls-Royce 6 a jere, take ya biya kuɗinsu, bisa sharaɗin wannan mutum da ya yiwa Sarki wulaƙanci, shi zai kai waɗannan motocin birnin Alwar na Indiya.
Jin haka kuwa, mamallakin wannan kamfani bai yi wata-wata ba ya amince, saboda cinikin da aka masa ya kai kimanin Biliyan 1 da miliyan 560 (1.5 billion) a kudin Nijeriya a yau. Tare da umartar wannan yaro da ya yi wa sarki wulaƙanci yaraka wannan motoci Indiya.
Motoci da dillali na isa fadar Alwar, Sarki Jai Singh ya bada umarnin a ƙirawo Sarkin Shara na Birni, domin ya tafi da waɗannan motocin a raba su a wuraren ɗibar shara.
Jin labarin cewa, a Indiya ana amfani da motar da tafi kowacce tsada wajen ɗibar shara, daga London a tura sakon bada hakuri da kyautar wasu Rolls guda 6 ga Sarki, kan a janye waɗancan motoci daga wajen aiki kwasar shara, domin hakan na iya zubarwa da kamfanin ƙima a idon duniya.
DARASI:
1.Mutum a matsayinsa na mutum, ba abin rainawa ba ne, kowaye.
2. Kar ka raina matsayin mutumin da baka san shi, ta iyu ya fi ka daraja a duniyance, ko a wajen Allah.
• MADOGARA:
Motoroid da Telegram
✍️Aliyu M. Ahmad
27th Dhul-Qaadah, 1443AH
27th June, 1443AH
0 Comments