1. Idan baka ji tsoron Allah, sai a sanya ma
tsoron bayinsa (mutane). Kullum kana baya, kana ganin kamar hassada, markici... ake kulla ma.
2. Idan baka yiwa iyayenka biyayya da kyautatawa ba, sai a jarrabe ka da bautawa wasu mutanen daban a banza. Sai a jarrabeka da soyayyar wata mata, ta yi ta wahalar da kai. Ko jarrabe ki da soyayyar wani namijin, ya yi ta wahalar da ke.
3. Idan baka yi amfani da dukiyarka da lokacinka wajen aikin alheri ba, a banza sai su kare a banza wajen aikin banza, daga baya kuma kana da-na-sani.
4. Idan baka gina kanka ba a lokacin kuruciya, sai ka yi da-na-sani a lokacin tsufanka.
5. Idan baka tsaya matsayin da Allah ya ajiye ka ba, zaka yi asara biyu. Na farko, ba zaka kai inda kake hankoro ba, na biyu; ka rasa tanadin da rayuwa ta ma.
6. Idan ka ɗauki karya da zamba tubalin gina rayuwarka ko wata alaka, tabbas ka jira shiga kunyar duniya da kiyama. Domin duk ginin da aka dasa harsashinsa da ƙarya, komai daren-daɗewa sai ya rushe.
7. Idan ka maida hankalinka wajen neman aibun mutane, zaka rasa lokacin gyara naka aibun da kurakurai.
8. Idan baka ɗaura damara cimma nasara ba, haƙiƙa ka daura damarar faduwa.
9. Idan baka tambaya ba, zaka ci gaba da zama da jahilci.
10. Idan baka motsa ba, zaka ci gaba da zama a inda kake.
✍️ Aliyu M. Ahmad
23rd Sha'aban, 1443AH
26th March, 2022CE
0 Comments