TABIN HANKALI

Akwai alamun 𝙩𝙖ɓ𝙞𝙣 𝙝𝙖𝙣𝙠𝙖𝙡𝙞 ga mutumin da ba shi da aiki kullum sai rubuta '𝙝𝙖𝙗𝙖𝙞𝙘𝙞' a social media idan muka yi duba ta fuskar نظرية التحليل النفسي na 𝙎𝙞𝙜𝙢𝙪𝙣𝙙 𝙁𝙧𝙚𝙪𝙙 (1856 - 1939).

Mu gane! 𝙏𝙖ɓ𝙞𝙣 𝙝𝙖𝙣𝙠𝙖𝙡𝙞 ba sai mutum yana yawo a birkice ba, cikin tsummokarai, yana surutai...; a'a, ciwo ne a kwakwale (اضطرابات نفسية ko 𝙥𝙨𝙮𝙘𝙝𝙤𝙡𝙤𝙜𝙞𝙘𝙖𝙡 𝙙𝙞𝙨𝙤𝙧𝙙𝙚𝙧) yana iya kama kowa ta wani sanadi, kamar cuttukan malaria, typhoid, ulcer da suke na zahiri (الأمراض الفسيولوجية). Wata jiyar, zaka yin ta a tafe, wata ko sai ta kwantar da kai, idan ta yi tsanani.

Daga cikin abubuwan da suke birkitawa mutane kwakwalwa, akwai zafin talauci, rashi ko mutuwa, cin amana, soyayya da sauransu (Rachman, 1978).

Yana ƙara bayyana a social media cewa, 𝙖𝙠𝙬𝙖𝙞 𝙢𝙪𝙩𝙖𝙣𝙚 (𝙙𝙖 𝙮𝙖𝙬𝙖) 𝙙𝙖 𝙨𝙪𝙠𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙞𝙣 𝙙𝙖𝙢𝙪𝙬𝙖, kuma ba su da hanyar bayyana damuwarsu face a social media. Masu irin waɗannan matsaloli, akwai buƙatar su je ganin likita (𝙥𝙨𝙮𝙘𝙝𝙤𝙩𝙝𝙚𝙧𝙖𝙥𝙞𝙨𝙩) domin ya taimaka musu da shawarwari da maganunuwa domin rage damuwa (Jeffrey, 2004). 

Daga cikin mafi sauƙin maganin rage damuwa, ko kuma shiga damuwa akwak, 𝙡𝙖𝙯𝙞𝙢𝙩𝙖𝙧 𝙯𝙞𝙠𝙞𝙧𝙞 (karatun Alkur'ani, Istigrafari, Salatin Annabi, dss) akai-akai, da kuma shagaltar da kai da wasu aiyukan (Ar-Ra'd, aya ta 28). 

Allah Ya yaye mana damuwa, Ya sanya salama cikin zukatanmu, amin.

✍️ Aliyu M. Ahmad 
18th Dhul-Qaadah, 1443AH
18th June, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #SocialMedia #FasaharZamani #Psychology #Hausa #Halayya

Post a Comment

0 Comments