Ita ce ✅ Itace ❌
Shi ne ✅ Shine ❌
Kai ne ✅ Kaine ❌
ƘA'IDA:
Ba a haɗe 'wakilin suna' (shi, ita, kai... da 'ne') a rubutu.
Misali:
• Ita ce matar zan aura
• Shi ne sabon gidan zan tare
• Kai ne babban abokin ango
(Kar ku ce lokaci ne ya kusa 😂, misali ne kurum)
Idan ka rubutu 'itace' maimakon 'ita ce', kalmar 'itace' suna ce, ma'ana 'icen dafa tuwo'.
A Hausa kuma, babu kalma 'shine' da 'kaine' don ba su da ma'ana har sai ka raba su da 'ne'.
-------------------------------------------
Ya yi ✅ Yayi ❌
Sun je ✅ Sunje ❌
Ta sha ✅ Tasha ❌
ƘA'IDA:
Ba a haɗa kalmar aiki/aikatau (mis. yi, je, sha...) da kowacce kalma (sai wasu wuraren).
Misali:
• Ya yi nasara a jarrabawa
• Sun je kasuwa
• Ta sha madara
Idan ka rubuta 'yayi' maimakon 'ya yi', kalmar 'yayi' suna ce, da iyu, 'yáyì', na tarkace (stuffs), ko 'yàyì' na wani abu ake yayi (trending).
Sannan, idan ka rubuta 'tasha' maimakon 'ta sha', kalmar 'tasha' suna ce, ma'ana, 'tashar mota' ko 'tashar jirgi'.
Mu Hausawa ne!
Mu gyara rubutun Hausarmu.
✍️Aliyu M. Ahmad
14th Dhul-Qa'adah, 1443AH
14th June, 2022CE
Photo credit:
Wikimedia (Gidan Hausa)
#AliyuMAhmad #Hausa #Nahwu #Linguistics
0 Comments