HADDACE ALKUR'ANI KADAI

Haddace Alkur'ani kadai, ba zai zama hujja ba a ilimi har sai ka koyi ma'anoninsa. Ba zaka ji zakin tilawar Alkur'ani ba, sai kana tadabburi in kana karantawa, kana gane ma'anoninsa. 

Imam Suyuti رحمه الله a cikin Al-Itqan fi Ulum al-Qur’an ya zayyanu fannoni 15 da ya kamata mai son fahimtar ma'anonin Alkur'ani da sakwanninsa ya koya.

Daga cikin fannonin nan, akwai: Nahwu, Lugah, Sarfu, Ma'ani, Badi'a, Usuludin, Fikhu, Usulul Fikhi, Ilmul Kira'at, Asbabun Nuzul, Nasikh wal Mansuk, Adab, Sira, Shi'r da Usulut Tafsir.

Haddace Alkur'ani yana da falala sosai, a duniya da lahira. Kuma, komai nacin mutum! Ba kowa ne ke iya haddace Alkur'ani ba. Kuma ba dole ba ne sai kowa ya hadda ce shi, sai wanda Allah Ya so da falalarsa, amma kowa zai iya zama domin koyon ma'anoninsa.

Akwai kuskure da daliban Islamiyya da yawa suke, da zarar sun yi saukar Alkur'ani (Hadda ko Tarteel), sai su yiwa kansu 'graduating' na daina zuwa makaranta daukar karatu, suna gani kamar sun gama karatu saboda sun haddace Alkur'ani.

✍️ Aliyu M. Ahmad 
9th Dhul-Qaadah, 1443AH
9th June, 2022CE

Photo Credit: iStock

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Alkurani #Quran

Post a Comment

0 Comments