SOCIAL ENGINEERING
Social engineering wata dabara ce da masu kutse (hackers) ke yiwa mutane in suna son su karbi wani bayani a hannunka ta hanyar ‘phishing attack’ da nufin za su taimake ka, ko baka wata kyauta.
Misali, ‘social engineer(s)’ za su tuntube ka a social media, ko a waya, ko ta message, su yi ma albishir da cewa, kana cikin wadanda suka yi nasarar samun wani ‘tallafi’, ko ka sami ‘kyautar recharge card/data’, ko a za saka ka cikin wani ‘online meeting’…. da sauransu.
Kana cikin wannan murnar, za su ce ma, “akwai wani ‘code’ zai shigo wayarka yanzu, in ya shigo ka fada musu, saboda yanzu za a saka ka a cikin list ko za a ma activating.” Da zarar ka fada musu, za su canja ‘password’ da duk wani ‘login details/credentials’ na shafunka, su kuma kwamushe ma shafinka baki daya.
Magana ta gaskiya, babu wani website, hukuma ko gidan waya (MTN, AIRTEL, GLO..) da za su baka kyautar kuɗi, recharge cards ko data. Kuskure mutane suke wajen bayar da bayanansu a yanar gizo, wai za su sami wata kyauta, kana bawa scammers (mazanbata) kyautar bayananka ne, za su kuma iya amfani da shi, ko ba yau ba, a duk lokacin da suka ga dama don cutar da kai. Kar ka yi mamaki don an kwashe ma kuɗaɗe a banki, ko an hacking wani social media handle naka, duk ta wannan dalilin (ka karanta: bit.ly/3xaJR08).
Da zarar wani ya kira da nufin ba ka wata ‘bonanza’, ‘tallafi’, ‘free recharge card/data’ ko ‘online meeting’ ya ce ka bashi wasu lambobi, kar ka bashi. Don da zarar ka ba shi zai kwamushe ma ‘shafinka.’ Sannan ba kowanne 'link' ne in aka turo aka ce ka cike za a baka tallafi ne zaka tura bayananka (details/data) ba tare da tantancewa ba da kwadayin neman za a baka tallafin kudi, data ko kudin kiran waya (recharge card/airtime).
Ubangiji ya yi mana gargadi a Alkur’ani, cewa: "ولا تلقوا بأيديكم إلى التهلكة " Ma'ana, "Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka.” [Baqara, aya ta 195].
Allah Ya ba mu ikon kiyayewa,
Allah Ya tsare mu.
(c) Aliyu M. Ahmad
7th Ramadhan, 1443AH
8th April, 2022CE
#AliyuMAhmad
#FasaharZamani
#BeCyberSmart
#SocialEngineering
0 Comments