Algorithm a ilimin lissafi (Mathematics) yana taimakawa wajen gano yadda bayanai ke alaka da juna (Encarta, 2009). A social media, shafukan sada zumunta na amfani da ‘algorithm’ don saukakawa ma’abota amfani da ‘social media’ ba su abubuwan da ake tsammani (automated reasoning) suke bukata (user’s feed), ta hanya amfani da:
1. Kalmomin da muke yawan amfani da su a chatting, ko
2. Bincike (searching/browsing) a ‘social platform’ (kamar Facebook, Youtube, Instagram….) ko ‘searching engine’ (irin su Google, Bing, Yahoo…), ko
3. Mutane da shafukan da muke bibiya (following) ko da baka following nasu, ko yi musu ‘reaction’; ko kuma
4. Abin da wasu abokanmu (friends/followers) da muke yawan mu’amala da su a social media suke ‘yi’ ko ‘bibiya’.
Kamfanonin sadarwar zamani (social media platforms) na amfani da hakan ne don yiwa manyan kamfanoni tallace-tallace (ads). Kamfanin Facebook da sauran wasu ‘social apps’ suna bibiyar bayananmu ta hanyar amfani da fasahar ‘artificial intelligence (AI)’ (الذكاء الاصطناعي) wanda ke amfani da tsarin ‘Algorithm’ wajen binciko bayani (data mining) daga abubuwan da na ambata a sama (cookies, chatting, following….).
A takaice, kafin ka fara korafin ‘social media’ na baka abubuwan da ba su kamata ba, ka fara tuhumar kanka da;
1. Wadanne irin kalmomi kake ‘chatting’ da su a sirri?
2. Me kake ‘browsing’ a ‘social media’ (Facebook, Youtube…) ko a ‘searching engine’ (Google, Bing, Yahoo….) ko kuma
3. Su waye kake abota (frinding/following) da su a ‘social media’?
Tabbas! Akwai yiwuwar daya daga cikin wadannan dalilin su sabbaba dalilin bayyanar abubuwan da ka fi gani a ‘social media’ na tallace-tallace, trending, scrolling…. Sai a kiyaye!
Na farko, in muka yi duba da tsarin ‘data broker’ ko ‘IB’ (dillancin bayanai), misali mu yi duba daga ‘chatting’ da muke a ‘Whatsapp’ ko kuma ‘browsing’ a ‘Google’ a kan ‘mota’ ko ‘computer’ ko ‘abinci’ ko ‘karatu’, Kalmar 'mota' ta yi daidai da abin da kamfanoni ‘Leventis Motors’, ‘Innoson Motors’ da su ‘Kaura Motors’ ke siyarwa (motoci), sai ka ga tallar motoci (sponsored). Ko kalmar ‘karatu’ ko ‘makaranta’ da a ‘timeline’ na Facebook, ko ‘feeds’ na Twitter, ko ‘scroll’ na Instagram da TikTok da sauransu.
ABUBUWAN LURA
1. A matsayinka na mai hankali, ka yi nazari, idan har wasu kamfanonin social media/platforms, suna iya bibiya tare da satar bayananka, da duk abubuwan da kake a social media a sirri, ina kuma ga Ubangijin da ya halicce ka, wanda Yake cewa: "وهو معكم أينما كنتم" Mana’a, “(Ubangiji ﷻ) Yana tare da ku a duk inda kuke” [Al-Hadid, 4], kuma Manzon Allah ﷺ yana cewa: “(اتق الله حيث ما كنت) كأنك تره فإن لم تكن تره فإنه يراك “ (Ka ji tsoron Allah a duk inda kake), kamar kana ganinsa, domin in kai baka ganinSa, to Shi yana ganinka.” [Bukhari, 50].
2. Da son ranka, ko ba son ranka; wajibi ne ka kiyaye daga kallon abin da shari’a ta haramta ma na alfasha a hotuna, bidiyo ko rubutu a social media ko zahirin rayuwa. Umarni ne daga Ubangiji ﷻ, cewa; "a fadawa mummunai maza da mata, su rika runtse idanuwasu, su kuma kiyaye al'aurarsu" [AnNur, aya ta 30].
3. Idan a ‘social platforms’ kamar ‘Facebook Reels’ ko ‘Tiktok’ ko ‘Youtube’ suna turo ma abubuwan da ba su dace ba, akwai matakin dakatar su. Kuma dama kamar ‘Facebook Reels’ da Tiktok ko ka so, ko ba ka so, dole za su ‘videos’ dake ‘treding’ a ‘scroll’, misali ‘Reels’ yawanci daga ‘Instagram ne’ amma akwai matakin dakatar su.
a. Akan ‘Facebook Reels’, ka shiga ‘Setting and Privacy’, sai ka shiga ‘Mobile Data Use’, zaka ga ‘options’ na ‘Autoplay’, sai ka dakatar da ‘autoplay’ na videos. Daga nan, babu wani video a ‘Facebook Timeline’, ko ‘Facebook Stories’ ko ‘Reels’ da zai ‘playing’ ba tare da ba shi izininka ba.
Ko kuma ka koma amfani da tsojon 'version' na Facebook (v.300.0.0.51.129) wanda ba a dora mahajar ‘reels’ ba, ko kuma kana amfani da browser kamar Chrome, Firefox, Opera, Edge dss., amma bana bada shawarar amfani da ‘third party Facebook app’ irin su SlimSocial saboda rashin tsaro.
b. A kan ‘Tiktok’ kuma, in sun nuno ma bidiyo maras kyau, ka yi ‘long press’ a kan videon, sai ka ‘click’ a kan ‘not insterested’ bidiyon zai bace kai-tsaye.
Na biyu, na yi kokarin ‘following’ na ‘users’ da suke yada alheri (mis. Malaman addini, motivational speakers, karatun Alkurani Maigirma...), domin su kasance kullum su ke (yawan) gilmawa a ‘scroll’ na Tiktok naka.
4. Mu kula da wandan ya kamata mu abota da su a ‘social media’, domin suna bada gudunmawa sosai wajen ganin wasu abubuwan da ko mun yi niyya, ko ba mu yi niyya ba saboda mu'amala da wadanda suke ta'ammuli da su. A cikin hadisi, Annabi ﷺ yana cewa: “Kwatankwacin zama da abokin kwarai, da mugun aboki kamar zama da mai sayar da turare (صاحب المسك) ne, da zama da makeri (وكير الحداد). shi mai sayar da turare ko dai ya sam maka, ko ka saya, ko kuma ka ji kamshi. Shi kuwa makeri ko dai ya kona maka sutura, ko kuma ka ji kauri”” [Sahih al-Bukhari, 2001].
5. Ba a yi social media don yada alfasha ba, sai dai ma'abota amfani da ita su yada alheri ko sharri yadda suka so. Social media kamar duniya ce da ubangiji ya halicce mu, wanda ya so ya shiryu, ya yi da’a; wanda ya so ya bata, sai ya kai kansa ga halaka.
✍️ Aliyu M. Ahmad
30th Shawwal, 1443AH
31st May, 2021CE
Photo Credit: Diib
#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Hausa #SocialMedia #Algorithm
0 Comments