TSAKANIN BADA TARBIYYA DA TAKURAWA

A matakin farko, iyaye su ya kamata su zama masu jin koken 'ya'yansu, su kuma jibanci lamuransu na rayuwa.

Tsakanin iyaye da 'ya'ya akwai hakkoki, ba iya na ciyarwa, ko biyan kudin makaranta, ko ba su wajen kwanciyya ba ne kadai, a'a... 'ya'ya suna da sauran hakkoki a kan iyaye.

Ibn Umar رضي الله عنه yake cewa: "إنما سماهم الله أبراراً لأنهم بروا الآباء والأبناء كما أن لوالدك عليك حقا كذلك لولدك عليك حقا." 

Idan ya kasance tsakaninka da 'ya'yanka ba jituwa, baka iya zama ka saurari damuwarsu; a'a, tsakaninka da 'ya'yanka kawai, daga FADA, HANTARA sai bada UMARNI, sai SANYA SU FARGABA da TSORO, babu WASA da DARIYA, babu JA A JIKA... to tabbas 'ya'yanka za su nesance ka, har lokacin da kake tsananin bukatarsu (lokacin tsufa). Za su kuma maida abokansu sune abokan shawararsu a duk abin da ya taso musu na rayuwa. Idan ba a yi dace ba, wasu abokan, za su kai 'ya'yanka ga halaka.

Akwai bambanci tsakanin bada TARBIYYA da kuma TAKURAWA. Wasu iyayen 'takure' 'ya'ya suke, su hana su sakat, da sunan kulawa; wannan ba 'tarbiyya' suke yi musu su ba. A bada tarbiyya, ana duba yanayin zamani (yau) da kuma muhalli (wurin zama) domin samun daidaito wajen bayar da tarbiyya.

A wata nasiha, Imam Ali ibn Abi Talib (RA) cikin إغاثة اللهفان (M2/265) yake cewa: 

لا تربوا أولادكم كما رباكم أباؤكم فقد خلقوا لزمان غير زمانكم

"Kada ku yi renon 'ya'yanku kamar yadda iyayenku suka rene ku, domin an halicce su ne a wani zamani ba irin naku ba" 

Na biyu, yadda 'ya'yan zamani suke da wayewa ta abubuwa da dama, ya wuce yadda (wasu) iyayen ke tsammani. Shi ya sa wasu iyayen ke mamaki sosai, idan aka ce, wane yaronka/yarinka suna kaza-da-kaza.

Mu sani! Duk wayonka, tsawatarwa da kokarinka ba zaka iya shiryar da 'ya'yanka ba, sai Allah Ya so su da shiriya. Idan ka sanyawa 'ya'yanka tsoron Allah, ko baka nan ba za su aikata ba daidai ba. Idan ka sanyawa 'ya'yanka tsoronka, a gaban za su nutsu, amma a bayan idonka za su aikata abin da suka ga dama. Ana kuma neman taimakon Allah cikin haka.

Allah Ya shiryar mana da zuri'a.

✍️ Aliyu M. Ahmad 
5th Dhul-Qaadah, 1443AH
5th June, 2022CE.

#Iyaye #Tarbiyya
#RayuwaDaNazari
#AliyuMAhmad

Post a Comment

0 Comments