• Idan ka kai shekara 25 - 30 amma har yanzu a gidan iyayenka kake kwana, Happy Children Day!
• Idan har yanzu a gidanku kake karbar abin ci, da kudin kashewa, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kana karbar kudin aski, da kudin siyen data a wajen Mama, Happy Children Day!
• Idan har yanzu a gidanku ake ma dinkin sallah, Happy Children Day!
• Idan kana hawa layin mai indomie da daddare, ko kana tsame naman miya a gidanku, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kana tsome (tsoma biredi a cikin shayi), Happy Children Day!
• Idan kana turo hotonka wa mutane don su ma happy birthday, Happy Children Day!
• Baka da aure, kuma baka da budurwa, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kana yiwa budurwa kuka, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kana ɗaukan kuɗin Mama a bayan pillow, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kina faɗa da ƙawarki a kan saurayi, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kina tambayar saurayi kuɗin anko, Happy Children Day!
• Idan har yanzu baki da sana'ar da zaki biyawa kanki ƙananun buƙata, Happy Children Day!
• Idan har yanzu kina faɗa da ƙannan ki akan wanda zai riƙe remote idan ana kallo a gida, , Happy Children Day!
Za ku iya karawa da naku, barkwanci ne, a yi raha! Allah Ya karawa rayuwarmu albarka 🤲
✍️ Aliyu M. Ahmad
26th Shawwal, 1443AH
27th May, 2022CE
#AliyuMAhmad #ChildrenDay #Hausa
0 Comments