Zakkar Fidda kai (Zakkatul Fitr), sadaka ce da aka farlanta domin tsarkake mai azumi daga kurakurai da yi a cikin watan Ramadhan, tare da nuna godiya ga Allah, zumunci da kyautayi tsakanin musulmi.
Tana wajaba ne a kan iya mutumin da yake da abincin da ya fi ƙarfin cikinsa (mawadaci). Zai kuma fiddawa duk wanda yake ƙarƙashin ciyarwasa (mis. ‘ya’ya, mata, iyaye, yaran gida dss). Matashi mai ciyar da kansa kuma, zai fiddawa iya kansa ne kawai.
Ana fitar da SA’I (mudu 4/2.15kg) na abinci da mutanen gari suka fi ci (mis. Masara, shinkafa, alkama, gero/dawa dss a nan). Kamar yadda a lokacin Annabi mutanen yanki sahara suna amfani da sha’ir, dabino, alkama.
Ana iya fitar da ita da sauran kwana biyu, ko ɗaya kafin Idi, ko a safiyar Idi kafin a yi sallar idi (Ibn Umar: Abu Dawood, 1609). Ana kuma bawa rukunin mutane takwas (8) da addinin ya ce a bawa Zakka (Tauba, 60). An hikimta hakan ne domin tausasa zuciyar marasa ƙarfi, tare da wadata su da abinci a ranar Idi.
Saboda lalurorin rayuwa da kuma ci gaban zamani, Malamai sun bada fatawar za a bayar da kuɗi madadin abinci, in an kiyasta. Wannan shi ne a taƙaice, Allah shi ne mafi sani.
Allah ya karɓa mana ibadu da addu’o’inmu, amin. Fatan an sha ruwa lafiya.
© Aliyu M. Ahmad
28091441AH 21052020CE
0 Comments