Idin karamar Sallah (Eid el-Fitr) biki da ibada ne na Musulmi don nuna farin ciki da yiwa Allah godiyar kammala Azumin watan Ramadhan. Sunna ne mai ƙarfi (Mu'akkada) da ake yi a Musallah (wajen gari/fili) ko kuma a masallachi da gidaje (in akwai lalura).
Ana son mai niyyar tafiya idi yayi wanka, sanya tufafi masu kyau tare da sanya turare, cin abinci kafin fita, canja hanya yayin zuwa da komawa gida; tafiya a kafa (in babu takura) tare da yin kabbarori, da kuma sauraron huɗuba. An so a fita da mata da yara (in da hali).
Daga cikin akwai salon kabbarorin akwai “ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA’ILAHA ILLALLAH; WALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMD” da wasu sauran salon, kuma ana yi ne a bayyana ba a ɓoye ba.
Ana yin IDI ne (da zarar rana ta ɗago; gwagwadon lokacin Salar Walha) da sallah mai raka’a biyu babu adhan ko iƙama, tare da yi kabbara 7 (har da ta harama) a raka’ar farko. Kabbarori 5 a raka’a ta biyu (ba tare da ɗaga hannu ba); ana kuma yin huɗuba bayan an kamala (ban da masu yin idi a gida).
Ana taya juna murna da faɗin “TAQABBALLALAHU MINNA WA MINKU” ma’ana “Allah ya karba daga gareku da mu.”
Allah ya karba mana, ya maimaita mana, amin. Fatan an sha ruwa lafiya.
© Aliyu M. Ahmad
30091441AH 23052020CE
0 Comments