1. Za ka iya sauqe Alkur'ani komai lalacinka, idan a kullum zaka yi tilawar izu 6 (6 x 10 = 60). Ko baka karantawa, ka rika sauraro da mafi dadadan muryoyin Qurra'.
2. Za ka iya ciyarwa da #100, a kalla kowacce rana da dabino 1, ko pure 1 ga mai azumi 1. Inda hali, ka ciyar fiye da haka, daidai gwargwadon karfinka.
3. Kar ka yadda sallah jam'i tana wuce ka, in son samu ne, ka samu sahun gaba.
4. Kar ka tsalle duk wasu nafiloli da ake a kowacce rana:
• Kafin Asuba - raka 2 (raka'atul Fajr)
• Sallar Walaha (Salatud Duha) - a kalla raka 2
• Kafin Azahar - Nafila raka 4
• Bayan Azahar - Nafila raka 2
• Kafin La'asar - Nafila raka 2
• Bayan Magriba - Nafila raka 2
• Kafin Isha' - Nafila raka 2
• Tarawih (Asham) da Tahajjud
5. Kar kan tsallake Adhkar (zikiri) na 'safiya' da 'maraice.'
6. Ka takaita yawan surutu, a takaita amfani da wayar hannu, sai in ya zama dole. Ka shagaltar da harshenka da yawan zikiri (Hailala, Hauqala, Tashibi, Tahmidi, Istigfari da Salatin Annabi صلى عليه وسلم).
7. Ka guji jin raye-raye, wakoki da kade-kade ko kallon 'films'. Gwamma ka koma zama a majalissin Tafsirin Alkur'ani Maigirma domin sauraron ma'anonin Alkur'ani, ko sauraronsa ko da a wayar hannunka ne ko gidajen talabijin.
8. Bayan an sha ruwa, ka yi kokarin ziyartar 'yan uwa da abokan arziki, da niyyar zumunci.
9. Mace ko tana cikin lokacin al'ada, kar ta yi wasa da lazimtar Adhkar, karatun Alkur'ani tare da addu'o'i kan bukatunta.
10. Addu'a ibada ce mai girma, mu yi kokari ribatar wannna lokacin wajen mika bukatunku ga Allah. Mu yi addu'a cikin ladabi, kankan da kai, yabon Ubangiji, farawa da Salatin Annabi صلى الله عليه وسلم, rokan ma iyayenmu, 'yan uwanmu da abokanmu gafara, shiriya da alherin duniya da lahira.
Kada ka jinkirta duk wani aikin alkhairi da zuciyarka ta ƙudurta yi zuwa wani lokaci ko gobe, inda da hali ka aiwatar da shi 'YANZU' kafin ka rasa damarka (RAI ko LAFIYA). Manzon Allah ﷺ yana cewa: “akwai ni’imomi guda biyu (2) wadanda da yawan mutane suna tozarta su (ba sa amfani da su, sai babu su kuma mutum yana nadama), sune ni’imar LAFIYA da LOKACI (Bukhari, 6049).
Ubangiji ﷻ yana cewa cikin Alqur’ani Maigirma, Ali-imran aya ta 133:
وسارعوا إلى مغفرة من ربكم وجنة عرضها السموات والأرض أعدت للمتقين
“Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda faɗinta daidai da sammai da ƙasa ne, an yi tattalin ta domin masu tsoron Allah.”
Mu yi kokarin ribatar abin da ya rage mana na kwanaki da lokaci a Ramadhan na bana da ibadu, neman gafara da addu’o’i kafin ya kubuce mana, don ganin na badi (shekara mai zuwa) sai mai kwana.
Muna rokon Allah Ya mana afuwa, Ya karbi ibadunmu, Ya amsa mana addu'o'inmu, amin.
اللهم اجعنا في العشر الأواخر من رمضان من عتقائك من النار، وارزقنا قيام ليلة القدر أيمان واحتسابا يا رب العالمين 🤲
(c) Aliyu M. Ahmad
21st Ramadan, 1443AH
22nd April, 2022CE
0 Comments