KU RIKA BIYAN MASU YI MUKU AIKI A KAN LOKACI

 #Ramadaniyyat 010



Bayan mun yi Sallar La'asar jiya, mun gabatar da nasiha a Masallacin Total kan abubuwan da suka shafi ibada a cikin Ramadan.


Fitowata daga masallaci ke da wuya, wani mutum ya tare ni a hanya. Idonsa kawai zaka kalla ka san cewa yana cikin yanayi na damuwa sosai.


Ya ce: "Don Allah Malam ku rika yiwa mutane wa'azi da nasiha kan  su rika biyan mutane hakkinsu in sun yi musu aiki, musamman a wannan yanayin."


Ya ce: "Ni ba sana'a ce ba ni da ita ba, ba kuma bara ko roko zan yi a masallaci ba. Ina da sana'ata, ina aikin birkilanci (bricklayer), da ita na dogara, nake daukar dawainiyyar rayuwata, da ta iyalina, har wasu ma na leburanci su ci a jikina.


A yanayin da nake ciki yanzu, yau na yi kwana 3 ina yiwa wani mutumi aikin birkilanci a gidansa, kullum sai ya ce gobe zai ban hakkina, har yanzu goben bani hakkina bata yi ba. 


Na farko: 

Ya tare ni a masa aiki, bai bar ni na je na yiwa wadanda zan yiwa aiki su iya biya na hakkina a kan lokaci ba.


Na biyu:

Ina da iyali, ga kuma azumi, yau kwana 2 ba a dora tukunya a gidana. Iyalina tana hakuri da ni, har ta fara zargin ina mata karya, saboda kullum ina fita aiki, amma zan dawo gida a gajiye, kuma babu ko sisi, ba cefene, sai abin da na dan kakkarumo a waje.


Na uku:

Yaron da muke aiki da shi, shi ma har ya fara korafi, yana zargi, gani yake kamar ana ban kudinsa ina cinyewa ne....


Malam! Ga azumi, ga zafi, ga gajiyar aiki, ba kudi, komai ya yi tsada, ga matsalar iyali, ga matsalar yarana da muke aiki da su... ni ban iya bara ko roko ba... 


Bai karasa maganar ba, ya girgiza kai, da alamun hawaye na kokarin fita a idonsa, ya sunkuyar da kai, ya yi shiru... 🥺 Ya salam!


---------------------


Duk da ban uzurin da ya hana wancan mutumin hana wannan bawan Allah hakkinsa ba, gaskiya akwai takura matuka, ka rikewa mutum hakkinsa ba, kuma magidanci mai iyali, ga azumi, ga zafin rana, ga tsadar rayuwa har na tsawon kwanaki 3 yana ma aikin karfi cikin rana, amma baka ba shi ko anini. 


Akwai wani hadisi na Abdullahi bin Umar رضي الله عنه, cewa Manzon Allah صلى الله عيه وسلم ya ce: 


أعطوا الأجير أجره قبل أن يجف عرقه


"Ka biya ma'aikaci ladansa (tun) kafin guminsa ya bushe" a wata ruwayar 'حقه' hakkinsa. [Ibn Majah].


A cikin رياض الصالحين Imam An-nawawi ya kawo wani na Imam al-Bukhari, hadisi na 1587; cewa, Annabi صلى الله عليه وسلم ya ambaci wasu mutum 3 ba-shi-ba-su a ranar tashin Alkiyama, cikin har da wanda yake hana wadanda ya saka aiki, ya hana su hakkinsu. "ورجل استأجر أجيرًا، فاستوفى منه، ولم يعطه أجره‏". 


A wani hadisin kuma na Abu Hurairah رضي الله عنه, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم  ya ce: "Rashin biyan bashi (a kan lokaci) ga mutumin da ke da halin biya, zalunci ne." 


Akwai takaici, akwai tausayi! Wasu mutanen fa, ko ba hakkinsu ne a kanka ba, dama can suna bukatar taimakonka, in ka yi duba izuwa yanayin rayuwarsu. 


Irin wadannan mutane kuma, su ba suna nema ko tara kudi ne don yin sutura ba, ko kera gida, ko siyan wasu kayan alatu ba; bal! Suna aiki tukuru ne don rufa kansu da iyalansu asiri. In sun shiga kunci, ba su iya roko ko bara ba, sai dai su yi ta samun matsala a cikin gidajensu. 


Don Allah mu daure mu daina jefa mutane kunci, ko ba zaka taimaki mutum ba, kar ka jefa shi cikin kunci. 


Ya Rabbi sallim, sallim 🤲!


✍️Aliyu M. Ahmad

10th Ramadan, 1443AH

11th April, 1443AH




Post a Comment

0 Comments