" الحكمة ضالة المؤمن أنى وجدها فهو يأخذها/أحق الناس بها"
[Jami` at-Tirmidhi 2687]
Harshenmu, bajon mu ne!
Da yawanmu, ba mu lura ko!
Wani abu da mai hankali ya kamata ya lura da shi, a yayin da muke ‘hakaito’ magana a kan wasu ko, wallahi furucinmu na nuna asalin mu ɗin su wa ye da kuma irin gidan da muka fito.
Cikin azumin nan, akwai wani lokaci da wani bawan Allah ya same ni, jikinsa na bari, ya ce zai ban labari. Na ce “Tom! Ina sauraro.”
Sai ya ce: “Kai wato Allah ya rufawa bayi asiri! Amma jiya na ga wani abin mamaki, a cikin watan Ramadan din nan, wasu kamar na Allah, abin fa ya ban mamaki, amma kasan inda na ga wane (*****) kuwa jiya da daddare? Babu wani susu da kai... Kai dai ga mutum kawai…”
Na yi shiru kadan ina tunani, sai nima na tambaye shi:
"TO KAI ME YA KAI KA WAJEN, HAR KA GAN SHI, A KUMA IRIN WANNAN LOKACIN?"
1. Yanzu kai ka ce min, wane (*****) ya je wurin wata alfasha, da daddare, cikin watan azumi (Ramadan), ba lalle na yarda ba, don ‘ni’ ban gan shi da ido na ba; amma kai, ka tabbatar min da kai ka je. Ka fallasa kanka kenan.
2. Da ma a duk lokacin da wani yana neman laifin wasu, sai basirarsa ta toshe, ya manta da kansa, yana hangen laifin wasu.
Anas bin Malik رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace: “كلُّ بني آدم خَطَّاءٌ وخيرُ الخَطَّائِينَ التوابون”, ma’ana "Dukkan 'ya'yan Adam masu kuskure ne, kuma mafifitan masu kuskuren, su ne masu tuba." [Tirmidhi 2687].
Na ce: “In ma ya tabbata yana laifi, ba ka tsammanin, a cikin daren jiyan, ya tashi cikin dare ya roki Allah gafara, kuma Allah ya gafarta masa? Don laifinsa, tsakaninsa da Ubangijinsa ne. Kai kuma abin nan da kake, akwai hakkinsa ciki [Jami’ul Ulum wal Hikam 18/199].
3. Ko ya je, ya yi abin da kake zarginsa da yi, ko bai je ba; kai yanzu a wajen Allah, kana da dayan manyan laifuffuka (kaba’ir) guda biyu:
• Na farko, in ya kasance da gaske ya je wajen da kai ma ka je din, to ka yi ‘gulmarsa’ (ghiba).
• Na biyu, idan ya kasance bai je ba, ka fada min ne don ka bata masa suna, to ka yi masa ‘sharri’ (buhtan) [Sahih Muslim, 2581].
4. Na ji labarin shi wannan da kake ban labarin na san, ya yi rabon kayan azumi, kuma cikin wadanda suka samu, har da kai; me yasa baka zo ka fada min wannan alherin ba? Me ya sa kuke boye alherin mutane, kuke gaggawar bayyana sharrinsu?
Allahu ﷻ ya ce: “والذين يؤذون المؤمنين والمؤمنات بغير ما اكتسبوا فقد احتملوا بهتانا وإثما مبينا” Ma’ana, “Kuma wadanda suke jifar (cutar) muminai maza da muminai mata, ba da wani abu da suka aikata ba, to, lallai sun dauki kiren karya da zunubi bayyananne.” [Ahzab, aya ta 58].
5. Abin da kake, mummuna zato ne, yana daga cikin kyawawan dabi’un Musulmi yiwa dan uwansa kyakkyawan zato: Allah ﷻ ya ce: “يا أيها الذين آمنوا اجتنبوا كثيرا من الظن إن بعض الظن إثم ولا تجسسوا ولا يغتب بعضكم بعضا أيحب أحدكم أن يأكل لحم أخيه ميتا فكرهتموه واتقوا الله”. Ma’ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashen zato laifi ne. Kuma kada da ku ke bincitar laifin wani , kuma kada sashenku ya yi gulmar sashe.” [Hujrat, aya ta 12]
Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: “إياكم والظنَّ، فإنَّ الظنَّ أكذب الحديث”. Ma’ana: “hane ku da zato domin shi zato shine mafi karyar zance.” [Sahih Muslim, 2563]
6. A je ma yana abin da kake zarginsa a kai, ka san Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: “من رد عن عرض أخيه رد الله عن وجهه النار يوم القيامة” ma’ana, “Duk wanda ya kare mutuncin dan uwansa, Allah zai kare masa fuskarsa daga wuta a ranar Alkiyama.” [Jamiat Tirmidhi, 1931]
A wani hadisin kuma: “من ستر مسلما ستره الله في الدنيا والآخرة”, ma’ana “duk wanda ya suturta (rufa asirin) wani Musulmi, Allah zai suturta (laifukansa) a duniya da lahira” [Sahih Muslim, 2699].
Ba ka mamakin garin ka tona asirin wancan bawan Allah, kai kuma naka asirin ya tonu? Domin kuwa da ba ka je wannan wajenba ba zama kasan ya je ba. Ba kuma nima zan san ka je ba.
SAI YA YI SHIRU, YA SUNKUYAR DA KAI KASA… YA NUNA NADAMA!
Don Allah mu gyara halayyarmu!
Mu daina kokarin tona sirrin asirin bayi, wanda Allah ya boye. Rufin asiri, na Ubangiji ne, a lokacin da kake kokari tonawa wani asiri na laifin dake tsakaninsa da Mahaliccinsa, a lokacin kai ma zaka yaye wani hijabi na abin da kake boyewa baka sani ba.
Allah ya gafarta mana abin da ya gabata, ya kuma shirye mu baki daya.
© Aliyu M. Ahmad
12th Ramadan, 1443AH
13th April, 2022CE
2 Comments
Amin y hayyu y qayyum
ReplyDeleteAllah y saka d Alkhairy, Allah qara Imani. Mun gode d abin alkhairy d kake mana. Allah biya d gidan jannatul firdausi
Allah Ya saka da Alkhairi
ReplyDelete