'Yar uwata!
Tabbas soyayya
jarrabawa ce babba, takan iya kama kowa, ba tare da duban jinsi (namiji ko
mace), ko shekaru, ko asali, ko matsayi ba.
A addinance, ba laifi
ba ne don mace ta ga wani namiji, mai addini, dabi’u, hankali/nutsuwa da rufin
asiri ta gabatar da soyayyarta gare shi. Bal! A tarihin Musulunci, Nana Khadija
bint Khuwaylid رضي الله عنها ita ce
ta tura aminiyyarta Nafisah bint Maniyyah don ta bayyawa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم soyyarta gare shi, har Allah
ya kaddara aure tsakaninsu صلى الله عليه وسلم, ta kasance matarSa ta farko, kuma mahaifiyya ga ‘ya’yan Shi صلى الله عليه
وسلم guda 6 cikin 7.
Akwai kuma wasu
misalan na yadda wasu matan suke zuwa wajen Annabi صلى الله عليه وسلم da nufin son aurensa, kamar cikin
hadisin Sabitul Banani رضى الله عنه
cikin Bukhari da Jamiaat Tirmidhi.
A tsarin zamantakewa
da al’ada, duk yadda bugun so ya bugi zuciyar mutane, namiji ne ke gabatar da
soyayya ga mace, ba mace ga namiji ba.
Kamar yadda al'amura
suke a yau, shawarar da zan bawa 'YAR UWATA; kar ki yi la’akari da misalan da
aka bada a sama; mazan yau ba irin na da ba ne. Duk yadda SO ya kai ga bugun
zuciyarki, kar ki fara tunkarar ‘namiji’ da kalmomin SO, ki dai yi iya
dabararki, da duk yadda za ki iya jan hankalinsa, har ya kawo kansa da kansa. In
dai namiji ne, kuma ya ji zai so ki, da kansa ko abokansa za su tunzura shi ya
'approaching' ki da soyayya. Uwa-uba, ki gama da addu’ar neman dacen abokin
rayuwa na gari.
Duk da ba a taru an
zama daya ba. Amma da gaske, maza suna raina duk macen da ta fara tunkurarsu da
‘SO’. Kuma abu kadan zai hada ku, ya yi miki gori, komai daren dadewa. Ba kowa
ne ya san darajar mace ba. Wani ya sami labarin bawa abokai a majalisi, har ana
zuldenki in kin zo wucewa.
Na biyu, duk namijin
da ya kawo kansa gare ki a karan-kansa, ya kuma juri ‘jan aji’ irin na mata da
wahalhalun soyayya, sai ya fi daukar ki da muhimmanci da tsada.
Ni namiji ne, matashi,
kuma muna ganin yadda al’amura suke wakana. Mutunci ya fi komai ‘yar uwata!
اللهم لا تعلق قلوبنا بما ليس لنا، لكن لساننا تسبقنا. واجعل لنا فيما نحب يا رب نصيب وإن كان بقلوبنا حب شيء لا يرضيك فأخرجه ولا تكلنا إلى اختيارنا ولا إلى قوتنا لا حول لنا ولا قوة إلا بك.
(c) Aliyu M. Ahmad
15th Ramadan, 1443AH
16th April, 2022CE
2 Comments
Masha Allah
ReplyDeleteMasha Allahu... Abinda ka fada yayi maana sosai... ALLAH ya qara qwaqwalwa dan uwa.
ReplyDelete