KIYAYE HARSHE

 





Harshe, tsoka ce da Allah ya ni’imta mana don jin ɗanɗano da samar da sautin magana tare taimakawar wasu sassa. Shi ne halittar da da zarar ka yi amfani da shi za a iya fahimtar kai waye; mai ilimi ko jahili, mai gaskiya ko maƙaryaci, wawa ko mai tunani/hankali dss. 


Harshe yana iya ɗauka ka, yana kuma kaskantar da kai cikin ƙanƙanin lokaci. Wasu sun rasa mulki/aiki, auren ya rabu, wasu na fursuna, an rasa addini duk ta dalilin harshe. 


Harshen na iya kisa ba tare da an zubda jini ba, sa kuka ba tare da duka ba, haddasa gaba, ƙiyayya, yaƙi da jawo da-na-sani in ba’a ƙiyaye me za'a na furtawa ba. 


Mu'azu dan Jabal (R.A) ya tambayi Annabi ﷺ game da aikin da zai shigar da shi aljanna, da nisantar da shi daga wuta. Sai Annabi ﷺ ya ce: "KA KIYAYE HARSHENKA." Mu'az ya ce: "SHIN YANZU ZA A KAMA MU DA ABIN DA MUKE FURTAWA? Sai Annabi ﷺ: “BA KOMAI KE AFKAR DA MUTANE TA KA (upside down) KO TA FUSKOKINSU CIKIN WUTA BA FACE ABUBUWAN DA HARSUNANSU SUKA GIRBA MUSU". [Tirmizi, 2616].


Matuƙar ba zaka faɗi alkhairi ba, gwamma ka yi shiru. Ƙarya, ƙazafi, gulma, annamimanci, sheda zur duk dangi ne na MANYAN ZUNUBAI. Idan baka ƙaurace musu ba zaka gami da fushin Allah, da kuma kunyata ka tun a nan duniya. 


(c) Aliyu M. Ahmad

30091441AH 

23052020CE

Post a Comment

0 Comments