Ikhlasi



Ikhlasi (yin aiki domin Allah) ɗaya ne daga cikin manyan sharuɗɗan karɓar aiyukan bayi a wajen Ubangiji bayan al-mutaba'a (yi gwargwadon yadda aka umarta). 


Riya (yi domin mutane su yaba) kuma, ita ce kishiyar ‘Ikhlasi’, ita kuma ake ƙira da 'شرك الأصغر (ƙaramar shirka).'


Wajibi ne dukkan wani aiki da ɗan Adam/Musulmi  zai yi, ya sanya ‘Ikhlasi’, ya yi domin neman yardar Allah kadai, ba don neman a mutane su yi masa 'yabo' ko 'jinjina' ba.


Domin, duk aiyukan alheri na; sadaka ko bada taimako, tilawar Alkur'ani, zumunci, nafiloli, ciyarwa da sauran dangogin aiyukan alheri da za ka yi, matukar domin neman yarda ko yabon mutane kake yi, KA YI SU A BANZA, kuma BABU LADA, gwamma kar ka yi.


Sai ka zo a ranar Alkiyama da aikin alheri lodi-lodi, sai ya maido ma da kayanka, a ce ka koma wajen wadanda ka yi domin su (mutane) su baka ladan aikin. 

 

Ibn Qayyim Al-Jawzy رحمه الله a cikin 'Arrooh' yana cewa:


فإن الله جعل الإخلاص والمتابعة سببا لقبول الأعمال فإذا فقد لم تقبل الأعمال .


Ma'ana: "Allah ya sanya ikhlasi (yin aiki domin Allah) da mutaba'a (yin aiki yadda aka ce) su zama dalilin karbar ayyuka, idan babu su, ba za a karbi ayyukan ba."


Mai yabonka ba shi da Aljanna a hannunsa, haka mai kushe ka ba shi da wuta a hannunsa. Mu yi ƙoƙarin nesanta ibadunmu da Riya. Ka 'YI' ko kuma ka 'QI YI' ba don neman yardar kowa ba sai ta Allah. Duk aikin alkhairi da ba IKHLASI ciki, wahalar banza ce.


اللهم ارزقنا الإخلاص في النية والسداد والتوفيق في القول والعمل


©️ Aliyu M. Ahmad

14th Ramadan, 1443AH

15th April, 2022CE

Post a Comment

0 Comments