Bayyana Soyayya ga Namiji

 




'Yar uwata!

 

Tabbas soyayya jarrabawa ce babba, takan iya kama kowa, ba tare da duban jinsi (namiji ko mace), ko shekaru, ko asali, ko matsayi ba.

 

A addinance, ba laifi ba ne don mace ta ga wani namiji, mai addini, dabi’u, hankali/nutsuwa da rufin asiri ta gabatar da soyayyarta gare shi. Bal! A tarihin Musulunci, Nana Khadija bint Khuwaylid رضي الله عنها ita ce ta tura aminiyyarta Nafisah bint Maniyyah don ta bayyawa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم soyyarta gare shi, har Allah ya kaddara aure tsakaninsu صلى الله عليه وسلم, ta kasance matarSa ta farko, kuma mahaifiyya ga ‘ya’yan  Shi صلى الله عليه وسلم guda 6 cikin 7.

 

Akwai kuma wasu misalan na yadda wasu matan suke zuwa wajen Annabi صلى الله عليه وسلم da nufin son aurensa, kamar cikin hadisin Sabitul Banani رضى الله عنه cikin Bukhari da Jamiaat Tirmidhi.

 

A tsarin zamantakewa da al’ada, duk yadda bugun so ya bugi zuciyar mutane, namiji ne ke gabatar da soyayya ga mace, ba mace ga namiji ba.

 

Kamar yadda al'amura suke a yau, shawarar da zan bawa 'YAR UWATA; kar ki yi la’akari da misalan da aka bada a sama; mazan yau ba irin na da ba ne. Duk yadda SO ya kai ga bugun zuciyarki, kar ki fara tunkarar ‘namiji’ da kalmomin SO, ki dai yi iya dabararki, da duk yadda za ki iya jan hankalinsa, har ya kawo kansa da kansa. In dai namiji ne, kuma ya ji zai so ki, da kansa ko abokansa za su tunzura shi ya 'approaching' ki da soyayya. Uwa-uba, ki gama da addu’ar neman dacen abokin rayuwa na gari.   

 

Duk da ba a taru an zama daya ba. Amma da gaske, maza suna raina duk macen da ta fara tunkurarsu da ‘SO’. Kuma abu kadan zai hada ku, ya yi miki gori, komai daren dadewa. Ba kowa ne ya san darajar mace ba. Wani ya sami labarin bawa abokai a majalisi, har ana zuldenki in kin zo wucewa.

 

Na biyu, duk namijin da ya kawo kansa gare ki a karan-kansa, ya kuma juri ‘jan aji’ irin na mata da wahalhalun soyayya, sai ya fi daukar ki da muhimmanci da tsada.

 

Ni namiji ne, matashi, kuma muna ganin yadda al’amura suke wakana. Mutunci ya fi komai ‘yar uwata!

 

اللهم لا تعلق قلوبنا بما ليس لنا، لكن لساننا تسبقنا. واجعل لنا فيما نحب يا رب نصيب وإن كان بقلوبنا حب شيء لا يرضيك فأخرجه ولا تكلنا إلى اختيارنا ولا إلى قوتنا لا حول لنا ولا قوة إلا بك.

 

(c) Aliyu M. Ahmad

15th Ramadan, 1443AH

16th April, 2022CE


Post a Comment

2 Comments

  1. Masha Allahu... Abinda ka fada yayi maana sosai... ALLAH ya qara qwaqwalwa dan uwa.

    ReplyDelete