Nazari: Ita Hausa kam ba yare ba ce?

 


A abin da aka koyar da mu a 'Falsafar Harshe' dukkan yaruka daya suke (all languages are equally valid). Kuma dama asali amfanin yare shi ne isar da sako (communication) (Sapir, 1921). Babu wani yare da yake da fifiko a kan wani, sai dai wajen amfani; misali Larabci saboda da addini, Turanci saboda kimiyya, fasaha, aiki da kuma cudayya da sauran mutane.


Yare ni'ima ce da Allah ya bawa mutum don ya rika mu'amala da wasu mutanen, don a cikin dabbobin da Allah ya halitta a ban kasa, mutum shi kadai ne ke iya sarrafa yare (specie-specific). Duk wata fasaha da za a yi a wani yare, za a iya yi a wani; domin hikima da baiwa 'universal' (na kowa da kowa) ce, ba a ware wasu mutanen daban ba. 


Mutum a karan kansa 'mortal rational animal' ne. Yare ba shi ne ma'aunin cewa wane fasihi ko kwararre ba ne, a'a; muna dai amfani da yare ne wajen bayyana baiwarmu da fasaharmu, ba don yare ba, babu wanda zai san mene ne zurfin tunaninmu, ya muka fahimci rayuwa, mene muke so dss (Fromkin et al, 2003). 


Tom! Amma abin da nake mamaki, in ka bi rubututtuka da ake social media, da za ka duba 'posting' 100 a 'timeline' da wuya ka samu 5% - 10% da suka yi rubutu da Hausa ba tare da sun yi mata lahani ba, ta fuskar nahawu (grammar), musamman wajen rarraba kalmomin aiki, suna, mallaka... da kuma wajen rubuta wasu kalmomin (orthographical error).


Amma da zaka yi rubutu da Larabci ko Turanci, ka dan baude, yanzu zaka ji an yi maka caaaa! To ita Hausa ba yare ba ce?


Don mutum ya yi 'blunder' (kuskure) a wani yaren ma fi masa uzuri, fiye da a ce a yarensa ne, a tawa fahimtar. Don babu wanda ya isa ya yi amfani da wani yaren da ba nasa na asali ba (mother tongue) ba tare da an samu tasirin L1 cikin L2 ba; ya danganta a kwarewar mutum. 


(c) Aliyu M. Ahmad

21st Rajab, 1443AH

23rd February, 2022CE

Post a Comment

0 Comments