“Abu ne mai kyau, a duk lokacin da ka dawo daga wajen aiki ka zauna lissafa riba da ƙalubale da ka samu yau. Anan zaka nemi hanyoyin warware da kaucewa ƙalubalen a gobe, tare da tunanin ɗabbaka hanyoyin ci gaba” (M. Kappel, 2017)
A ɗayan hannun kuma, Sayyadina Umar (RA) na cewa:
"حاسبوا أنفسكم قبل أن تحاسبوا، وزنوا أنفسكم قبل أن توزنوا"
“KU YIWA KANKU HISABI TUN KAFIN A YI MUKU HISABI, KU RIƘA AUNA AIYUKANKU KAFIN A AUNA MUKU” [Ighathatu al-Lahfan 1/145]
Abu ne mai kyau yiwa kanka da kanka hisabi kafin kwanciya bacci (a kowane dare) na abin da ya shafi alakarka Ubangijinsa (ibada), mutane (mu’amala) da ma karan-kanka da tananinka da misalan tambayoyi kamar haka:
• Ya ka gudanar da sallolinka na yau? A kan lokaci, cikin jami’i ko wanin haka.
• Shin ka karanta ko sauri wani sashi na Alƙur’ani Maigirma a yau? Adkhar fa?
• Ya alakarka da mutane?
• Ya kake sarrafa harshenka? Shin kana amfani da shi wajen yaɗa ko faɗin alkhairi, ko kuwa yi maganganun karya, gulma, tsurku, annamimanci, cusa haushi dss?
• Ya tsaftar kuɗaɗen da ka samu a yau? Akwai riba, yaudara, cuwa-cuwa dss?
Haƙiƙa! Sunna ce ta mutanen kirki yiwa kai hisabi a lokacin kwanciya. Yiwa Allah godiya da neman dace a inda aka yi daidai da kulla niyya yi azama a gobe. Neman gafara da yin nadama a wuraren da aka yi kuskure da yin niyyar kaucewa aikata kuskuren a gobe.
Ka auna! Idan sharrinka ya fi alkhairinka yawa, ka ɗaura damarar komawa ga Allah. Idan alkhairinka ya fi sharrinka yawa, ka ƙara neman kusanci zuwa ga Ubangiji. Mutuwa tana hanyar zuwa ɗaukarka a kowane lokaci.
Allah (SWT) na cewa: “Ku bi Allah da taƙawa, kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe… lalle Allah Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa” [Hashir; 18].
Allah Ya sa mu dace.
© Aliyu M. Ahmad
05121441AH 26072020CE
0 Comments