Duk wani abu mai muhimmaci a rayuwarka ka rika boyewa, ka rika sirrintawa: neman aure, aiki, yawan dukiyarka, matsalar cikin gida/iyali, tafiya, wani shiri da kake don cimma wani buri.. kishin wasu ke jira su dagulama al'amari, walau mai kyau, ko mummuna.
Za ku yarda da ni in na ce muku, a lokuta da dama mu muke jawowa kanmu mahassada, ko barayi; saboda rashin sirrinta wasu falolin Allah a kanmu; tabbas ido gaskiya ne, kuma akwai shaidanun mutane.
Idan ka fadawa amininka sirrinka, ka sani shi ma yana da amini; wanda ba lalle ya kansace masoyinka ba ne.
Amininka da zuci daya zai je majalissa yana bada labarin falolinka, ko dukiyarka ko wani shiri da kake don cimma wani buri a rayuwa. Wannan in ba a yi sa'a ba zai zama 'unintentional informant' ga mugayen mutane; barayi dss.
Imam Ali (RA) yana cewa: "masoyanka mutum 3 ne, haka nan makiyanka mutum 3 ne. Masoyinka masoyinka ne, kuma masoyin masoyinka, sannan makiyin makiyinka. Makiyinka kuma makiyinka ne, makiyin masoyinka, kuma masoyin makiyinka." Ko ka so, ko ka ki, wani da kake so, amini ne ko dan uwa ga wanda yake ma adawa.
Don kana abu da zuciya daya; baya nufin don akuya ba ta ci kura ba, kura ba zata ci akuya ba. Balarabe yana cewa: الخصوصية قوة، فالناس لا يستطيعون تدمير ما لا يعرفونه. Alhaji, 'privacy is power.'
NB:
Aikata rashin gaskiya ba ya daga ciki, domin duk daren dade asirin maras gaskiya na bayyana.
(c) Aliyu M. Ahmad
22nd Rajab, 1443AH.
24th February, 2022CE.
0 Comments