Misali, idan ka bawa mutum 2 matasa kowannensu kyautar ₦100k. Idan ɗayan ya kafa sana'a, ya juya, ya samu ribar ₦30k a wata, zuwa watan gaba yana da ₦130,000. Shi kuma ɗayan, in ya yi facaka da ₦70k, ya ɗinka sutura, ya je yaje wuraren nishaɗi, ya ɗauki hotuna, ya watsa a social media, zuwa ƙarshen wata yana da ₦30 kenan 😌.
A zahiri, mutum na biyu an fi masa kallo ya yi nasara a rayuwa, saboda yadda ya bayyana a socia media, da son shuhura, fariya da burge mutane. Amma a haƙiƙa, mutum na farko shi ne ya yi gadon kai, saboda ya ɗauki hanyar gina kansa, kuma a kwan-a-tashi, zai yi rayuwa irin wacce mutumin farko ke fata, in arziƙi a juyu ya ginu.
GASKIYAR LAMARI
Wani abu da zai baka mamaki da rayuwarmu, mu matasa; saboda gaggawa da son rayuwar hutu, mu kan ga ₦100k ta mana ƙaɗan mu kafa jari (saboda raina sana'a), amma bama ganin yawanta wajen shagali da son fariya da burge mutane.
Bai isheka mamaki ba 🤔 matashin da ke riƙe da waya ƙirar iPhone ta kusan ₦200k, kuɗin siyan data yana gagararsa, kuma ma wai yana ma ƙorafin ya rasa aikin yi, bayan ga jari nan a hannunsa.
Rayuwar duniyar nan, ba wanda baya son hutu, kayan alatu (luxuries), da nuna izza. Amma duk waɗannan sai an yi gumi ake samunsu. Ko ba ka yi gumi ba, dole ne wani ya yi gumi, ka sha romon gumin nasa.
A KAN RAINA SANA'A
A addinance, dole ne akan kowanne mutum ya fita nema daga falalar Allah, ta halastacciyar sana'a don rufa kai asiri (Hadith). Muna da tarihin wasu daga cikin Annabawan Allah, sahabbai, salihan bayi da manyan mutane da irin yadda suka yi gwagwarmaya a rayuwarsu. Wasu sun yi kasuwanci da fatauci,wasu noma, su da kiwo, aikin ƙarfi da fikira, wasu sunyi sana'o'in hannu irinsu su ƙira (walda a zamanance), ɗinki da saƙa, da sauransu.
Kamar Annabi Idris (AS) ya yi ɗinki/telanci (tailoring). Annabi Nuh da Annabi Zakariyya (AS) sun yi sassaƙa, wacce zamu iya cewa kafintanci (carpentry) a zamanance. Annabawa da yawa sun yi sana'ar noma kayan abinci, kamar Annabi Ayyub, Shu'aib da Uzairu (AS). Annabi Yunus (AS) Ya yi sana'ar su (kamin kifi). Annabi Yusuf da Harun (AS) ma'aikatan gwamnati ne. Annabin Rahama ﷺ, Annabi Musa, Yaqub, Ishaq (AS) duk sun yi kiwon dabobbi. Hatta cikin mata, ga Uwar mummunai, Nana Khadija (RA), attajira ce, babbar ƴar kasuwa.
An taɓa tambayar Manzon Allah ﷺ kan wacce sana'a ce tafi, ya ce: "wacce mutum ya yi da hannunsa". Kuma Manzon Allah ﷺ ya yi bushara ga talaka (maras komai) mai girman kai (عائل مستكبر) da cewa; yana cikin mutum 3 da Ubangiji ﷻ ba zai musu magana ba, ba zai tsarkake su ba, ba zai kalle su ba a ranar Alƙiyama (Sahih Muslim).
Allah Ya sanya mana albarka cikin nemanmu,
Allah Ya horewa waɗanda suke neman madogara daga falalarsa.
Amin.
(c) Aliyu M. Ahmad
13th Muharram, 1442AH
22nd August, 2021CE
0 Comments