Jiya da Yau

A wata nasiha, Imam Ali ibn Abi Talib (RA) cikin إغاثة اللهفان (M2/265) yake cewa: 


لا تربوا أولادكم كما رباكم أباؤكم فقد خلقوا لزمان غير زمانكم


"Kada ku yi renon 'ya'yanku kamar yadda iyayenku suka rene ku, domin an halicce su ne a wani zamani ba irin naku ba" 


Wannan maganar! Ta cancanci malamai su sanya ta cikin hudubar Juma'a, wuraren wa'azantarwa da guraren karatuttuka; cewa duniyar yau, 2000s ta sha bamban sosai da 1900s zuwa baya. 


Ka ga illar 

rashin jan 'ya'ya a jiki, 

rashin fahimtar me ke damunsu, 

ko mai suke so, 

wane irin tunani suke game da rayuwa... abubuwa ne da iyaye ya kamata su lura su fahimta game da 'ya'yansu, musamman a yau.


Maimakon a ce kana mahaifin 'ya'yanka, ka zame musu Aljanna, bango, inda za su kai kukansu... sai ya kasance in ka shigo gida, duk sai su ji su a takure, kamar 'yan fursun, da sunan kar a rainka. Tom! In ya kasance tsakaninka da 'ya'yanka babu kyakkyawar magana, daga 'bada umarni' da 'sai fada', kar ka zargi kowa don sun dasawa kwakwalwarsu wani tunani, ko sun dauko wata mummunar dabi'a ta daban musamman a duniyar yau.  


'Ya'yanka za su fara shaye-shaye har ya zame musu jiki (addict) ba tare da ka sani ba. Hana su kuma ya gagare ka, saboda ya zame musu dabi'a.


'Yarka zata zama karuwar gida, baka sani ba, baka san wadanda take mu'amala da su ba; har sai in wani rikici ya tashi ne, tukun zaka iya sani.


Saurayin 'yarka ya fika sanin yanayin al'adarta, da sauran matsalolin mata, hasali ma ya kasance shike dawainiyya da ita in wani abu da ya shafi hakan ya taso.


'Yarka ta yi sabo da da wani (a soyayya), har ta yi nisa, sai lokacin da ka so aurar da ita ne, zaka so bata umarnin ta so abin da kake so, ita kuma ta bijera ma.


Da wasu misalan ma da dama...


Wannan zamanin ya zo da sauye-sauye, na mugun son kudi, son holewa, wayewa, son burga...  da yawa cikin matasa da yara masu tasowa, haka suka fahimci rayuwa. 


Misali! Idan yaro ko yarinya suna da tunanin son a burge, kuma babu kudi, yarinya zata iya siyar da mutuncinta don ta samu kudin hada 'birthday party' ko 'siyan anko'. Kar ka dauka yarinya sai ta yi nauyi (ciki) tukun ta zama 'yar iska, suna da sabbi dabaru.


Haka in yaro ya fara shaye-shaye, har ya zama 'addict' wallahi in ta motsa bai 'afa' 'tsotsa' 'zuka-da-busawa' ko 'kurba' ba, zai iya sata ko daukar kayan kowaye ya siyar don ya samu nutsuwa da abubuwan shaye-shaye. Zai yi wuya ka kama barawo ko mai kidnapping, ko dan kungiyar asiri baya shaye-shaye. Shi ma shaye-shayen yau ba sai an bugu ana tangadi ba, irin na da... laifin da kuma wanda ake sabawa sune ababen dubawa... 


In ka cewa 'da/'ya su bi Iyaye, sai ka tambaya, shin an ba su tarbiyyar daukar wannan maganar? Ka ga dabi'ar shaye-shaye, zina, shaukin so...


Sai ka rasa ina zamu je, wacce irin al'umma za a samar a gobe; mu ba tarbiyya Islamiyyar ba, ba ta al'ada ba, ba ta Turawan ba. Ga mu da son 'ya'ya, kin karbar laifi, kuma a hankali sai sun farauci duk mai hakkin kula da tarbiyya a karshe. 


Zaman lafiya da ci gaban al'umma tana cikin tarbiyyar al'umma da kuma irin tunanin da suke. Iyaye kuma sune 'kamfanin' samar da al'ummar da duniya zata wayi-gari da su a gobe. 


Allah Ya shiryar mana da zuri'a.


(c) Aliyu M. Ahmad

2nd Rajab, 1443AH

4th February, 2022CE




Post a Comment

0 Comments