Iyaye


Inda mun san yadda iyayenmu suke jin dadi da farin ciki a cikin zukatansu idan mun yi abin kirki, abin a yaba; da kullum mun rika kokarin aikata alheri ko don farin cikinsu.

Da kuma mun san yadda zukatan mahaifanmu ke tafasa in an kawo musu labari ko sun gani da idonsu muna aikatawa wani abu na rashin da'a, wallahi ko don su ma rika nesanta jikinmu daga abin da zai bata musu rai, ya sa su cikin damuwa.

A matsayinka na da, ko'ina ka shiga a fadin duniyar nan, tamkar wakilin gidanku/mahaifanka kake a duk inda ka samu kanka. Duk abin da ka yi, na kirki ko na tsiya; duniya za ta ba su 'credit'.

Na kan sha mamaki irin yadda muke kokarin nuna bajinta tare da nuna girmamawa ga malamanmu a makarantu, iyayen gidanmu a siyasa ko a wajen aiki; amma mu manta da wadanda suka yi sanadin zuwanmu duniyar da har muka samin wadancan damar, suma suna bukatarmu fiye da kowa. 

Ai ko ba zaka yi abin da sai iyayenka su yi alfahari da kai ba, ya sanya su cikin farin ciki, tom! Ka rika kokari kaucewa abin da zai sa su bakin ciki, jawo musu zagi, ko kunyar duniya; balle har su yi da-na-sanin haihuwarka.


(c) Aliyu M. Ahmad

29th J/Awwal, 1443AH

1st February, 2022CE


Post a Comment

0 Comments