Wadatar Zuci

Farin cikin yana cikin wadatar zuci (self content) ba cikin mallakar ababen 'kawa (luxuries) ba.


Rashin wadatar zuci ke bude yawancin kofofin barna, kama daga

sata, 

cin bashi na ba gaira-ba-dalili, 

garkuwa da mutane, 

danne hakkin wasu, 

ci hanci... 


Rashin wadatar zuci ke sa neman dukiya ta kowacce hanya, yaki halal, yaki haram.


Rashin wadatar zuci ke sawa zukata tsatsa, har zuciyar ta gamu cutar yiwa wasu hassada don kana jin wani ya fika da wata ni'ima ta duniya.


Rashin wadatar zuci ke sa, sai ka ga wanda ya fika abin duniya zai nemi ya danne ka don shi ya samu. Wani ko da duk dukiyar duniyar nan zaka tara masa, baki daya, in ya samu dama sai ya cuceka.


A kullum gasarka a rayuwa, ka takaita ta tsakanin kai kanka ne a jiya da kuma yau, ka kuma godewa Allah dubba ni'imominsa da ya yi ma, hakan zai sa ka rayuwa cikin farin ciki, ba tare da burin sai ka fi wani, ko ka yi rayuwa irin ta wani ba.


Shi ya sa a cikin wani hadisi, Manzon Allah صلى الله عليه و سلم ya mana umarni a duk lokacin da muka tashi duban ni'imomin da Allah ya mana, mu yi duba ga wadanda suke kasa da mu, sai mu godewa Allah; amma sa zarar mun yi duba ga wadanda suka fi mu, sai mu raina, mu kuma cika zukatanmu da buri [Muslim, 2963]. 


Farin ciki ba siyan sa ake ba, bai kuma liko kan mallakar kawa (luxuries) ba, jin sa ake a zuci. 


Allah Ya kara mana wadatar zuci. Ka sanya mu cikin bayinka masu godiya da arzikin da ka bamu, kada ka sanya mu cikin bayinka masu gasa, kwadayi da son abin duniya har mu shagala mu manta dalilin da ya sa muka zo duniya (neman yardar Allah).


(c) Aliyu M. Ahmad

28th J/Awwal, 1443AH

31st January, 2022CE




Post a Comment

0 Comments